Isra’ila ta aikata laifukan yaƙi bayan tilastawa Falasɗinawa barin gidajensu – HRW
Ƙungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch, ta zargi hukumomin Isra’ila da yin sanadiyar tilastawa Falasɗinawa barin gidajensu daga Gaza, wanda ya kai ga zama laifukan yaƙi da cin zarafin bil’adama.
Rahoton da ƙungiyar ta fitar a Alhamis ɗin nan, shi ne na baya-bayan a jerin waɗanda ƙungiyoyin agaji na ƙasa da ƙasa suka fitar, wanda ke gargadi game da mummunan halin da ake fuskanta na gudanar da ayyukan jin kai a yankin da aka yi wa ƙawanya.
Human Rights Watch ta gano cewar an tilastawa mutane yin gudun hijirar ya zama ruwan dare a yankin, wannan kuma laifukan cin zarafin bil adama ne.
Kawo yanzu dai hukumomin rundunar sojojin Isra’ila da na ma’aikatar kula da harkokin wajen ƙasar, basu ce komai kan wannan lamari ba, duk da cewa a baya mahukuntan ƙasar sun yi watsi da irin waɗannan zarge-zargen, inda suka ce dakarunsu na gudanar da ayyukansu ne bisa tsarin dokokin ƙasa da ƙasa.
Dokokin yaƙi na ƙasa da ƙasa dai sun haramta korar fararen hula daga yankunan da aka mamaye, sai dai idan ya zama dole saboda baiwa fararen hula kariya ko kuma dalilai na soji.
A shekarar data gabata ne dai Isra’ila ta ƙaddamar da mamaya a yankin Gaza, bayan da mayaƙan Hamas suka kai hari a yankunan kudancin ƙasar, inda hukumonin Isra’ilan suka tabbatar da mutuwar mutanenta kusan 1 da dari 2 tare da yin garkuwa da sama da 250.
A hare-haren ramuwar gayya da Isra’ila ta kaddamar a yankin Gaza, sama da mutane dubu 43 ne hukumomin lafiyar Gaza suka tabbatar da mutuwarsu tare da tilastawa kusan miliyan 2 da dubu dari 3 barin muhallansu, lamarin da ƙungiyar ta Human Rights Watch ce wani ƙirƙirarren al’amari ne.