An samu rudani yayin da kamfanin man fetur na kasa NNPCL ta kori manyan jami’an ta Ajiya da Eyesan

Spread the love

Kamfanin man fetur na Najeriya NNPCL, ya sanar da sauye-sauye ga hukumar da tayi a tsakanin manyan jami’ansa, inda aka sauke Umar Ajiya da Oritsemeyiwa Eyesan daga mukamansu na babban jami’in kudi da mataimakin shugaban zantarwa na kamfanin.

A madadin su, NNPCL ta nada Isiyaku Abdullahi a matsayin sabon mataimakin shugaban zartarwa da Udobong Ntia. Hakanan, Adedapo Segun, wanda ya kasance an nada shi babban jami’in kudi.

A cikin wata sanarwa da kamfanin na NNPCL ya fitar a daren Larabar da ta gabata, ta ce nade-naden na da nufin inganta harkokin tafiyar da kamfanonin da kuma yadda ake gudanar da ayyuka, wanda hakan ke nuni da yadda kamfanin na NNPCL ya jajirce wajen samun nasara na dogon lokaci a fannin makamashin Najeriya.

Sanarwar da aka karanta a wani bangare na cewa, hukumar daraktocin kamfanin NNPCL Limited, ta yi farin cikin sanar da jerin nade-naden nadin shugabannin.

Waɗannan canje-canje suna nuna ci gaba da sadaukar da kai don haɓaka kamfani da
gudanar da mulki, dama inganta yadda ake gudanar da ayyuka, da kuma tabbatar da samun nasara na dogon lokaci a fannin makamashin Najeriya.

An yi muhimman nade-naden ne kamar yadda aka nada Mista Adedapo A. Segun a matsayin Babban Jami’in Kudi, Segun inda ya yi aiki a kamfanin kuma yabada da muhimmiyar gudunmawa ga ayyukan kamfanin, Isiyaku Abdullahi an nada shi mataimakin shugaban zartarwa.

Wadannan nade-naden sun yi daidai da kudurin kamfanin NNPC Limited na gina kyakkyawan jagoranci don fitar da ingantaccen aiki da tallafawa manufofin kamfanin na NNPCL.

Hukumar da Gudanarwa sun kuma mika godiyar su ga Umar Ajiya da Oritsemeyiwa A. Eyesan bisa sadaukarwar da suka yi ga kamfanin NNPC Limited.

Kamfanin NNPCL Limited ya ci gaba da jajircewa wajen ganin ya samu kyakyawan aiki, da inganta makamashin Najeriya a idon duniya, da tabbatar da dorewar kudi, tare da fifita muradun al’ummar Najeriya a harkar man fetur.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button