Cutar lassa ta halaka mutane 11 a jihar Benue – Kwamishina Lafiya

Spread the love

A ranar Litinin ne gwamnatin jihar Benue ta sanar da cewa jihar ta samu bullar cutar zazzabin Lassa guda 63, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 11 a bana.

 

Dokta Yanmar Ortese, Kwamishinan Lafiya na jihar wadda Dokta Joshua Agbadu ya wakilce shi, ne ya bayyana hakan yayin wani taron karawa juna sani na kula da cutar zazzabin Lassa a Makurdi, inda ya bayyana cewa an samu asarar rayuka 17%. Ortese ya bayyana ci gaban da aka samu wajen magance cutar amma ya jaddada bukatar ci gaba da samun horo. Ya kara da cewa ma’aikatan kiwon lafiya takwas ne suka kamu da cutar yayin da suke jinyar marasa lafiya.

 

Taron wanda ma’aikatar lafiya tare da hadin gwiwar hukumar NCDC da WHO suka shirya, an shirya shi ne don inganta dabarun magance cutar zazzabin Lassa.

 

Dokta Mohammed Abdulkarim, ko’odinetan hukumar ta WHO a jihar, ya jaddada kudirin kungiyar na magance cutar, yana mai bayyana ta a matsayin kalubalen kiwon lafiyar al’umma.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button