YANZU-YANZU: Tinubu ya soke aikin gyaran hanyar Abuja, Kaduna, Zaria zuwa Kano
Tinubu ya soke aikin gyaran hanyar Abuja, Kaduna, Zaria zuwa Kano
Gwamnatin Najeriya ta soke kwangilar gyaran hanyar Abuja-Kaduna-Zaria-Kano, Sashe na I (Abuja-Kaduna) daga kamfanin Julius Berger Construction.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya, Mohammed Ahmed, ya fitar a ranar Litinin.