Zan dawo da Kano zuwa APC – sabon Minista
Sabon Karamin Ministan Gidaje da Raya Birane Yusuf Abdullahi Ata, ya ce manufarsa ita ce dawo da jihar Kano jam’iyyar APC a shekarar 2027.
Ata ya bayyana haka ne jim kadan bayan ziyarar daya kai jahar Kano bayan an rantsar da shi a matsayin majalisar zartarwa ta tarayya.
Da yake zantawa da manema labarai, ya ce, “Nadin nawa ya samo asali ne saboda siyasa, APC ta rasa jihar Kano, kuma yanzu za ta dauki jihar Kano. Babban matsalar Kano ta tsakiya kuma ni daga can nake.
“Ko a matsayina na minista zan ci gaba da zama a wannan Unguwa, za mu yi aiki tukuru don ganin APC ta samu mulkin Jihar Kano nan da 2027.
Ata ya yabawa shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa wannan nadin, inda ya kara da cewa ba don kan sa ba, sai dai na ‘yan Kano da Najeriya ma.
Don haka ya tabbatar wa shugaban kasa cewa a 2027, Kano za ta koma APC.