Janye tallafin man fetur shi ne abu mafi kyau da ya faru a Nijeriya – Sanata Sani Musa
Sanata Sani Musa, shugaban kwamitin majalisar dattijai mai kula da harkokin kudi, ya ce cire tallafin man fetur shine abu mafi kyau da ya faru da Najeriya.
Musa ya bayyana haka ne a wata hira da gidan talabijin na Channels cikin shirinsu na Politics a ranar Juma’a.
Ya ce cire tallafin, zai ba wa yan kasuwa damar tantance farashin yadda suke so.
Sai dai Sanata Sani Musa ya ce hukumar ta NNPC tana gyara kura-kurai da ya faru a baya ne.
Sai dai da dama daga cikin yan Nijeriya na gani janye tallafin na daya daga cikin abin da ya jefa kasar cikin halin matsin tattalin arziki