Gwamna Abba Kabir na Kano, ya sake bude asibitin haihuwa Nuhu Bamalli.

Spread the love

A kokarinsa na rage mace-macen mata da kananan yara, Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sake bude asibitin mata masu juna biyu na Bamalli Nuhu bayan wasu gyare-gyare da gwamnatinsa ta yi.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Alhamis.

Da yake jawabi ga wadanda suka halarci bikin sake bude asibitin a ranar Alhamis, Gwamnan ya bayyana jin dadinsa da inganta ginin.

Ya kara da cewa bayan hawansa ofis, asibitin yana cikin tabarbarewar yanayi kuma daya daga cikin wuraren da ya fara ba da fifiko domin inganta shi.

Gwamna Yusuf ya bukaci masu ruwa da tsakin asibitin da su kula da sabbin kayan aikin da aka girka tare da tsaftace wurin, inda ya jaddada muhimmancin samar da ingantaccen kiwon lafiya ga mazauna Kano.

Ya kuma tabbatar wa al’ummar jihar cewa gwamnatin sa ta himmatu wajen samar da ingantaccen kiwon lafiya.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button