Gwamnatin Tububu ta ware biliyan27 don rabawa tsofaffin shugabannin kasa

Gwamnatin Tububu

Spread the love

Gwamnatin tarayya ta ware zunzurutun kudi har naira biliyan 27 domin biyan tsofaffin shugabannin kasa, mataimakan su, shugabannin kasa na mulkin soji, shuwagabannin ma’aikata masu ci da wadanda su ka ritaya da kuma malaman jami’a da suka yi ritaya a kasafin kudin 2025, kamar yadda wani bincike da jaridar PUNCH ta gudanar a yau Asabar ya nuna.

Wadanda za su ci gajiyar wannan kason sun hada da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, Goodluck Jonathan, da Muhammadu Buhari, da Umaru Musa Yar’adua tare da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, Namadi Sambo, da Farfesa Yemi Osinbajo.

Sauran wadanda ake sa ran za su ci gajiyar kuɗaɗen sun hada da tsohon shugaban kasa na soja, Janar Yakubu Gowon (mai ritaya) da kuma Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya), da kuma tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Ibrahim Babangida da babban hafsan sojin kasa, Commodore Ebitu Ukiwe mai ritaya da sauran su.

A ranar Laraba ne dai shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da kasafin kudin 2025 sanya kai N49.70tn a gaban majalisun taraiya.

Rundunann soji

Rundunonin sojin Najeriya sun yi wa manyan hafsoshi ƙarin girma

Jaridar trustradio ta rawaito cewa

Rundunonin sojin Najeriya sun yi wa ɗaruruwan manyan hafoshin ƙarin girma a wani mataki na inganta ƙwazon aiki.

Cikin wata sanarwa da rundunar sojin ƙasa ta ƙasar ta fitar ta a shafinta na X, ce ta yi wa manyan hafsoshi 35 masu muƙamin Birgediya Janar ƙarin girma zuwa matsayin Manjo Janar, sannan ta yi wa masu muƙamin Kanal 73 ƙarin girma zuwa matsayin Birgideiya Janar.

A nata ɓangare ita ma rundunar sojin sama ta ƙasar ta sanar da yi wa manyan hafsoshi 19 zuwa matsayin Air Vice Marshals, sannan ta yi hafsoshi 33 ƙarin girma zuwa Air Commodores.

Labarai masu alaka

Hukumar kwastam ta kama buhunan shinkafa, man fetur, da suka kai naira miliyan 229 a iyakar jihar Ogun

 

Sai kuma rundunar sojin ruwa da ta yi wa manyan hafsoshinta 146 ƙarin girma.

Rundunar sojin ruwan ta ce ta ƙara wa hafsoshi 24 girma zuwa ‘Rear Admiral’, sai 26 zuwa matsayin Commodore, da kuma 96 da aka ƙara wa girma zuwa matsayin ‘Captain’


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button