Rundunonin sojin Najeriya sun yi wa manyan hafsoshi ƙarin girma

Rundunar Soji

Spread the love

Rundunonin sojin Najeriya sun yi wa ɗaruruwan manyan hafoshin ƙarin girma a wani mataki na inganta ƙwazon aiki.

Cikin wata sanarwa da rundunar sojin ƙasa ta ƙasar ta fitar ta a shafinta na X, ce ta yi wa manyan hafsoshi 35 masu muƙamin Birgediya Janar ƙarin girma zuwa matsayin Manjo Janar, sannan ta yi wa masu muƙamin Kanal 73 ƙarin girma zuwa matsayin Birgideiya Janar.

A nata ɓangare ita ma rundunar sojin sama ta ƙasar ta sanar da yi wa manyan hafsoshi 19 zuwa matsayin Air Vice Marshals, sannan ta yi hafsoshi 33 ƙarin girma zuwa Air Commodores.

Labarai masu alaka

Hedikwatar tsaron Najeriya ta musanta kafa sansanin sojin Faransa a Najeriya 2024

Sai kuma rundunar sojin ruwa da ta yi wa manyan hafsoshinta 146 ƙarin girma.

Rundunar sojin ruwan ta ce ta ƙara wa hafsoshi 24 girma zuwa ‘Rear Admiral’, sai 26 zuwa matsayin Commodore, da kuma 96 da aka ƙara wa girma zuwa matsayin ‘Captain’


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button