Jihohin Najeriya da suka fi tara kuɗaɗen haraji a 2023
Muhawara game da jihohin da suka fi tara kuɗin shiga a Najeriya ba sabuwa ba ce, amma maudu'in ya ƙara zafi tun bayan da Shugaban Ƙasa ya bijiro da batun gyaran dokar karɓa da kuma rarraba haraji a ƙasar.
Muhawara game da jihohin da suka fi tara kuɗin shiga a Najeriya ba sabuwa ba ce, amma maudu’in ya ƙara zafi tun bayan da Shugaban Ƙasa ya bijiro da batun gyaran dokar karɓa da kuma rarraba haraji a ƙasar.
Babban abin da ya fi jan hankali a ƙudirorin dokar huɗu da ke gaban majalisar dokoki shi ne yadda za a dinga karɓar harajin VAT da kuma hanyoyin da za a dinga raba shi tsakanin jihohi 36 na ƙasar – da kuma birnin Abuja.
Baya ga kason kuɗaɗen da gwamnatin tarayya ke bai wa kowace jiha duk wata, kuɗaɗen da jihohin ke tattarawa daga haraji da sauran hanyoyin samu kan ba su damar gudanar da ayyukan raya ƙasa, da kuma biyan basukan da suke ci. Daga BBC Hausa.
Yayin da masana da ɗaiɗaikun ‘yan Najeriya ke ci gaba da muhawara kan ƙudirorin dokar na Tinubu, mun duba jihohin da suka fi tara haraji da kuma kuɗin shiga a cikin gida a shekarar 2023.
Mun samu bayanan ne daga rahoton da hukumar ƙididdiga ta ƙasa National Bureau of Statistics (NBS) ta fitar a watan Oktoban 2024, wanda ya ba da alƙaluma daga 2020 zuwa 2023.
Bayanan sun ƙunshi manyan hanyoyin samu biyu na kowace jiha. Su ne kuɗaɗen da ake karɓa a matsayin haraji, da kuma wanda gwamnatocin ke samu daga ayyukan da hukumominta ke aiwatarwa.
Wannan maƙala ta duba ɓangaren harajin ne kuma a shekarar 2023 kawai. Duka lissafin kuɗaɗen na kuɗin Najeriya ne wato naira.
Jihohi 10 da ke kan gaba
Legas
Rahoton na NBS ya ce jihar Legas Jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya ta tara jimillar kuɗi daga haraje-harajen da ta karɓa a 2023 naira biliyan 704,901,304,307.85.
Kazalika, ta samu jimillar kuɗin shiga biliyan 815,864,679,971.27 a shekarar.
Abuja
Babban birnin tarayya – wanda ba a ƙirga shi a cikin jerin jihohin Najeriya – ya tara jimillar kuɗin haraji naira biliyan 211,100,288,136.36 a 2023.
Kuma wannan adadin shi ne jimillar kuɗin shigar da ya samu a shekarar.
Rivers
Rivers da ke kudu maso kudancin ƙasar ta karɓi harajin da ya kai naira biliyan 186,967,541,813.09 a 2023.
Jimillar kuɗin da ta samu a 2023 kuma shi ne tiriliyan 195,414,581,585.34.
Delta
Jihar Delta da ke kudu maso kudanci ta karɓi biliyan 146,875,041,475.36 a matsayin kuɗin haraji cikin shekarar 2023. Sai kuma jimillar kuɗin shiga naira biliyan 114,088,309,224.99 da ta samu.
Ogun
Jihar Ogun tana yankin kudu maso yammacin Najeriya, kuma ta samu kuɗaɗen haraji naira biliyan 71,678,001,198.73 a 2023.
Jimillar kuɗin shiga kuwa sun kai biliyan 146,875,041,475.36.
Kaduna
Idan muka tsallaka yankin arewa maso yamma, jihar Kaduna ta tara naira tiriliyan 49,025,168,057.44 a matsayin kuɗaɗen haraji a 2023. Kazalika ta samu kuɗin shiga jimilla biliyan 62,490,117,635.22.
Edo
Jihar Edo ma a kudu maso kudanci ta samu jimillar naira biliyan 46,170,315,748.87 na kuɗaɗen haraji, da kuma jimillar kuɗin shiga biliyan 64,671,497,361.77 a 2023.
Oyo
Kuɗin harajin da jihar Oyo a kudu maso yamma ta tattara sun kai jimillar biliyan 40,526,520,039.70, sannan ta samu biliyan 52,745,497,059.04 a matsayin kuɗin shiga a shekarar 2023.
Kwara
Jihar Kwara a arewa ta tsakiya ta samu jimillar biliyan 23,129,511,652.06 a kuɗaɗen haraji, da kuma 59,642,678,119.83 na jimillar kuɗin shiga.
Akwa Ibom
A 2023, jihar Akwai Ibom a kudu maso kudancin Najeriya ta samu kuɗaɗen haraji da suka kai biliyan 36,072,272,694.13, ta kuma samu jimillar biliyan 43,184,024,626.77 a matsayin kuɗin shiga.
Ina Kano ta shiga?
Jihar Kano da ta fi kowacce yawan al’umma a arewacin Najeriya, ita ce kuma kan gaba a harkokin kasuwanci da tattalin arziki.
Sai dai ba ta cikin 10 na farko wajen tattara kuɗaɗen haraji da ma kuɗaɗen shiga a 2023, kamar yadda alƙaluma suka nuna a sama.
A 2023 ɗin, Kano ta karɓi kuɗaɗen haraji naira biliyan 30,533,943,698.70 ne kawai, inda ta samu biliyan jimillar kuɗin shiga biliyan 37,379,619,998.26.
Hakan ya sa ta zama ta 12 a jerin jihohin Najeriya mafiya samun kuɗin shiga a 2023.
Sai dai kuma a 2022, jihar da ke arewa maso yamma ta samu jimillar kuɗin shiga 42,509, 911,699.94 (fiye da na 2023 kenan), amma kuma harajin da ta tattara na biliyan 30,187,194, 255.58 bai kai na 2023 (30,533,943,698.70) ba.
Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, ya ce daga watan Nuwamban 2024 yawan albashin da jihar ke biya zai kai kusan naira biliyan bakwai duk wata – saboda sabon mafi ƙanƙantar albashi na N71,000 da za ta fara biya.
Dogaro da kai
Wani rahoto da cibiyar BudgtIT ta fitar a watan Oktoban 2024 ya nuna cewa jihohin Najeriya 31 sun fi dogara ne kan kason kuɗin da suke samu daga gwamnatin tarayya.
Rahoton binciken ya sanya jihohin Rivers, da Legas, da Anambra, da Kwara, da Cross River a matsayin waɗanda suka fi ƙarancin dogaro da kuɗin da suke karɓa daga kasonsu na gwamnatin tarayya a 2023.
“Hakan na nufin halin da za a shiga [idan babu kason kuɗi daga Abuja] ba zai ma misaltu ba,” in ji Malam Abubakar Aliyu, wani masanin tattalin arziki a Najeriya.
“Ba za a iya biyan albashi ba, ba za a iya biyan ‘yan kwangila ba, ba za a iya samun kuɗin gudanar da gwamnati ba,” a cewarsa.
Cibiyar BudgIT ta ce waɗancan jihohin biyar ne kaɗai ke da yiwuwar iya gudanar da harkokinsu da iya kuɗin da suke samu a cikin gida idan da a ce za su rayu ba tare da kaso daga gwamnatin tarayya ba.
“Sauran 31 dole ne sai sun gyara hanyoyin samun kuɗinsu kafin su iya yin wata rayuwa ba tare da kasafin kuɗi daga Abuja ba,” a cewar binciken BudgIT.
Jihar Kano da ta fi kowa yawan al’umma a arewacin Najeriya ta karɓi naira biliyan 16.328 a matsayin kasonta na watan Yulin 2024.