Sojoji sun wargaza sansanonin IPOB a jihohi 3 na Imo, Enugu, da Ebonyi
Sojojin Hadin Gwiwar Rundunar Kudu maso Gabas mai suna Operation UDO KA sun wargaza sansanonin kungiyar (IPOB) da bangaren da suka dauki makamai, wato Eastern Security Network (ESN), a jihohin Imo, Enugu, da Ebonyi.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Laftanar Kanal Jonah Unuakhalu, ya fitar a Umuahia ranar Lahadi, wanda aka isar ga manema labarai.
Kamfanin dillancin Labarai ta Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa sojojin sun hada da rundunar Sojojin Kasa, Sojojin Ruwa, da Sojojin Sama tare da hadin gwiwar ‘Yansanda, DSS, da Hukumar Tsaro da Kare Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC).
Unuakhalu ya bayyana cewa, rundunar hadin gwiwa ta wargaza sansanin IPOB a Uhuala-Aku, karamar hukumar Okigwe ta jihar Imo ranar Juma’a.
Ya kara da cewa mambobin IPOB din sun gudu cikin rudani zuwa cikin daji mai makwabtaka sakamakon karfin wutar sojoji.
Tsohon gwamnan Neja ya bayyana hukuncin kisa ga masu kashe jami’an tsaro a kasar nan 2024
Sojoji sun lalata maboyar ƴan bindiga tare ƙwato makamai da oota a Taraba da Benue
Runduna ta 6 na Rundunar Sojan Nijeriya/Sashe na 3 na Operation Whirl Stroke (OPWS) sun samu gagarumar nasara a ci gaba da aikin soji na dawo da zaman lafiya da tsaro a Jihar Taraba da wasu sassan Jihar Benue karkashin shirin “Operation Golden Peace.”
A ranar 7 ga Disamba, 2024, jami’an sun gudanar da aikin kawar da bata gari da aka tsara sosai a yankunan Akahagu da China a Karamar Hukumar Ukum, Jihar Benue.
An ci gaba da aikin zuwa kauyen Ikayor, inda suka fafata da ‘yan bindiga a wani sansani da aka danganta da sanannen dan ta’adda da ake nema ruwa a jallo, Akiki Utiv, wanda aka fi sani da “Full Fire.”
A lokacin arangamar, sun yi amfani da karfin wuta mai yawa, wanda ya tilasta wa ‘yan bindigar tserewa cikin rudani da barin sansaninsu.
Bayan fafatawar, an kwato wata mota kirar Toyota Corolla ja da babur. A yayin binciken motar da aka bari, an gano wando na kamuflajin soji, bindigar Beretta tare da harsashi daya na 9mm, da wasu kayan daban.
Da yake magana kan aikin, Kwamandan Runduna ta 6, Birgediya Janar Kingsley Uwa, ya jinjinawa sojojin bisa jarumtaka da jajircewarsu duk da kalubalen da suke fuskanta. Ya kuma tabbatar wa mazauna Taraba da Benue karkashin Sashe na 3 na OPWS cewa sojoji za su ci gaba da kasancewa masu jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin.
Ya kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da bayar da bayanai masu inganci da na lokaci don taimakawa kokarin hukumomin tsaro.
Hukumar Kwastam ta samu mace ta farko da ta zama matukiyar jirgi
Mataimakiyar Sufuritanda Kwastam (Mai tukin Jirgi) Olanike Balogun ta kafa tarihi a matsayin matar farko da ta zama matukiyar jirgi a Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS), inda ta taka rawar gani wajen karya shingaye a fannin zirga-zirgar jiragen sama.
An haifi Balogun a Kaduna, kuma asalin ta daga karamar hukumar Odo-Otin, Jihar Osun. Tafiyarta ta fara ne a shekarar 2002 lokacin da aka dauke ta aikin Kwastam a matsayin Mataimakiyar Ma’aikaciya domin yin aiki a matsayin ma’aikaciyar cikin jirgi a sashen sufurin jiragen sama na hukumar.
Da take magana a wata hira kwanan nan, DSC Balogun ta bayyana yadda burinta mai karfi da tallafin Hukumar suka taimaka mata daga matsayin ma’aikaciyar jirgi zuwa samun lasisin zama matukin jirgi. Ta ce, “Tsayawa a Hukumar lokacin da yawancin abokan aikina suka koma wuraren da ake biyan albashi mai tsoka a kamfanonin jiragen sama babban kalubale ne, amma na jajirce don ba da gudunmawata ga hidimar jama’a tare da cimma burina na zama matukin jirgi.”
Nasorinta a aiki sun hada da samun Diploma mai zurfi a fannin Tikitin Jiragen Sama da Ayyukan Ma’aikatan Cikin Jirgi, Digiri na biyu a Fannin Gudanar da Jama’a daga Jami’ar Ahmadu Bello, da kuma samun takardar shaidar zama matukin jirgi daga Flying Academy a Miami, Florida, da Hukumar Kwastam ta dauki nauyin horon.
Shugaban Hukumar Kwastam, Adewale Adeniyi, ya yaba da jajircewar ta, yana mai cewa nasararta shaida ce ta yadda Hukumar ke ba da muhimmanci ga inganta ma’aikata da sabbin hanyoyin ci gaba. Ya ce, “Labarin ta yana nuna abin da za a iya cimmawa da jajircewa da kuma tallafin hukuma.”