‘Yan bindiga sun kashe manoma 7, an ƙone buhun masara 50 a Neja
Maharan sun kuma kashe wani mutum bayan karɓar miliyan 20 kuɗin fansa daga hannun iyalansa.

Aƙalla manoma bakwai, ciki har da wani ɗan agaji, ’Yan bindiga suka kashe, tare da ƙone buhun masara 50 a garin Bangi da ke Ƙaramar Hukumar Mariga a Jihar Neja.
Trust radio ta rawaito cewa, Shaidu sun ce manoman da ‘yan bindiga suka sace suna kan hanyar dawowa daga gonakinsu da motar da ta ɗauko masara, ‘Yan bindigan suka yi musu kwanton ɓauna.
‘Yan bindiga Sun kashe duk wanda ke cikin motar sannan suka ƙone motar tare da masarar.
Wani ganau ya ce, “’Yan bindigar sun jira har sai da manoman suka gama loda buhun masara 50 a cikin motar.
“Suna barin gonar, sai suka buɗe musu wuta, suka kashe su sannan suka ƙone motar tare da masarar.”
Manoma a Mariga suna shan wahala wajen girbin amfanin gonarsu, saboda hare-hare, kashe-kashe da satar mutane da ’yan bindiga ke yi a yankin.
A wani lamari kuma, ’yan ta’adda sun kashe wani mazaunin garin Kontagora, Malam Danjuma duk da karɓar kuɗin fansa Naira miliyan 20 daga hannun iyalansa.
Danjuma ya shafe makonni uku a hannun maharan kafin su kashe shi.
Wani mutum da ya tsere daga hannun ‘yan bindigar ya sanar wa iyalan Danjuma labarin mutuwarsa.
Yahaya Suleiman, wani mazaunin Kontagora, ya ce garkuwa da mutane ya zama ruwan dare a wasu sassan garin a ’yan makonnin nan.
Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da kashe manoman bakwai.
Ya ce, “A ranar 16 ga watan Nuwamba, da misalin ƙarfe 3 na rana, an yi wa mutum bakwai kwaton ɓauna, lamarin da ya yi sanadin mutuwar wasu daga cikinsu.”
Ya ƙara da cewa jami’an tsaro da suka haɗa da ’yan sanda da sojoji sun tura tawagarsu zuwa yankin don hana sake faruwar lamarin.
Yan Bindiga sun yi garkuwa da mutane 6 a Taraba
Rahotanni daga jaridar leadership sun bayyana cewa wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun kashe wani manomi tare da yin garkuwa da mutane shida a garin Garbatau da ke karamar hukumar Bali a jihar Taraba.
Yayin da rundunar ‘yan sandan ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance dangane da lamarin ba, majiyar mu ta tabbatar da cewa an kashe wani shahararren manomi mai suna Wanda Maibultu a gonarsa da yammacin ranar Asabar.
“Maibultu ta kasance fitaccen manomi ne wanda ya yi gagarumin aiki a kauyen Garbatau mai tazarar kilomita kadan daga garin Garba Chede,” in ji Adamu Dauda, wani mazaunin Maihula.
A cewar Mista Dauda, masu garkuwa da mutanen sun bukaci a biya su kudin fansa naira miliyan 100 daga iyalan manoman da aka sace. Rahotanni sun ce an dauke mutanen shida ne a lokacin da suke aikin girbin amfanin gona a kusa da Garbatau, wata al’ummar manoma da ke zaune a tsakanin tsaunuka biyu.
Wannan lamarin ba shi kadai ba ne; Mista Dauda ya lura cewa al’umma sun sha fama da sace-sacen mutane da dama a baya. A bara, an sace manoma da dama a wani samame daban-daban, inda aka tilastawa da yawa biyan kudin fansa domin a sako su.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Usman Abdullahi bai samu amsa ba, saboda bai amsa kira ko sako dangane da lamarin ba.
Satar mutane don neman kudin fansa ya zama ruwan dare a yankuna da dama na Taraba da wasu jihohin arewacin Najeriya, inda kungiyoyin da ke dauke da makamai ke yin wadannan ayyuka.
An bayyana harin da ‘yan bindiga ke yi wa manoma da kuma mamaye al’ummomin noma a matsayin muhimman abubuwan da ke haifar da matsalar karancin abinci a NajeriyaFarfesa Emeriti a taron na bana.
An dakatar da alkalai na babbar kotu a jihohin Rivers da Anambra
Hukumar Shari’a ta Ƙasa (NJC) ta dakatar da Mai Shari’a G. C. Aguma na Babbar Kotun Jihar Rivers da Mai Shari’a A. O. Nwabunike na Babbar Kotun Jihar Anambra daga gudanar da ayyukan shari’a.
An dakatar da su tsawon shekara guda ba tare da albashi ba, sannan za a sanya su a jerin wanda za a sanya ido a kansu na tsawon shekaru biyu bayan haka.
An yanke wannan hukuncin ne a taro na 107 na NJC wanda Babbar Mai Shari’a ta Najeriya, Kudirat Kekere-Ekun, ta jagoranta a ranakun 13 da 14 ga Nuwamba 2024.
Jimillar Alkalai guda biyar da ke kan aiki sun samu hukunci saboda aikata laifuka daban-daban na rashin da’a.
Hukumar ta kuma bada shawarar a tilasta wa wasu shugabannin kotuna biyu yin murabus saboda canza shekarun haihuwa.
An kai maroƙi kotu bisa zargin sace wayoyin abokan ango a wajen daurin aure
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta gurfanar da wani mutum mai suna Bashir Abubakar Brigade a gaban wata kotun shari’ar Musulunci da ke zamanta a Fagge ‘Yan Alluna bisa zargin laifin satar wayoyin abokan ango a yayin daurin aure.
Daily Trust ta rawaito cewa an kama Bashir ne bisa zargin satar wayoyin hannu guda biyu da kudinsu ya kai Naira dubu 125 da kuma Naira dubu 25.
Lauyan masu shigar da kara na Jiha, Barr. Zaharaddeen Mustapha, ya karanta wa wanda ake zargin laifukan da suka hada da hada baki da kuma sata.
Sai dai ya musanta zargin da ake masa, inda ya jaddada cewa shi ba barawo ba ne, maroƙi ne kawai.
Daga bisani kotu ta bada belinsa da sharadin ya kawo dan uwansa na jini da kuma takardar shaidar wani gida da ya mallaka.
Alkalin kotun, Khadi Umar Lawan Abubakar ya dage sauraron karar har zuwa ranar 25 ga watan Nuwamba domin bayar da shaida.
Yan Bindiga sun yi garkuwa da mutane 6 a Taraba
Rahotanni daga jaridar leadership sun bayyana cewa wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun kashe wani manomi tare da yin garkuwa da mutane shida a garin Garbatau da ke karamar hukumar Bali a jihar Taraba.
Yayin da rundunar ‘yan sandan ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance dangane da lamarin ba, majiyar mu ta tabbatar da cewa an kashe wani shahararren manomi mai suna Wanda Maibultu a gonarsa da yammacin ranar Asabar.
“Maibultu ta kasance fitaccen manomi ne wanda ya yi gagarumin aiki a kauyen Garbatau mai tazarar kilomita kadan daga garin Garba Chede,” in ji Adamu Dauda, wani mazaunin Maihula.
A cewar Mista Dauda, masu garkuwa da mutanen sun bukaci a biya su kudin fansa naira miliyan 100 daga iyalan manoman da aka sace. Rahotanni sun ce an dauke mutanen shida ne a lokacin da suke aikin girbin amfanin gona a kusa da Garbatau, wata al’ummar manoma da ke zaune a tsakanin tsaunuka biyu.
Wannan lamarin ba shi kadai ba ne; Mista Dauda ya lura cewa al’umma sun sha fama da sace-sacen mutane da dama a baya. A bara, an sace manoma da dama a wani samame daban-daban, inda aka tilastawa da yawa biyan kudin fansa domin a sako su.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Usman Abdullahi bai samu amsa ba, saboda bai amsa kira ko sako dangane da lamarin ba.
Satar mutane don neman kudin fansa ya zama ruwan dare a yankuna da dama na Taraba da wasu jihohin arewacin Najeriya, inda kungiyoyin da ke dauke da makamai ke yin wadannan ayyuka.
An bayyana harin da ‘yan bindiga ke yi wa manoma da kuma mamaye al’ummomin noma a matsayin muhimman abubuwan da ke haifar da matsalar karancin abinci a NajeriyaFarfesa Emeriti a taron na bana.
An kashe manoma 7, an ƙone buhun masara 50 a Neja
Maharan sun kuma kashe wani mutum bayan karɓar miliyan 20 kuɗin fansa daga hannun iyalansa.
Aƙalla manoma bakwai, ciki har da wani ɗan agaji, ’yan bindiga suka kashe, tare da ƙone buhun masara 50 a garin Bangi da ke Ƙaramar Hukumar Mariga a Jihar Neja.
Shaidu sun ce manoman suna kan hanyar dawowa daga gonakinsu da motar da ta ɗauko masara, maharan suka yi musu kwanton ɓauna.
Sun kashe duk wanda ke cikin motar sannan suka ƙone motar tare da masarar.