Kotu ta wanke Kwamishina daga jihar Jimawa bisa zargin lalata da matar aure

matar aure

Spread the love

Gwamna Namadi ya janye dakatarwar da ya yi wa Kwamishinansa bayan kotu ta wanke shi

Gwamna Malam Umar Namadi ya dage dakatarwar da aka yi wa Kwamishinan ayyuka na Musamman, Auwalu Dalladi Sankara, daga yanzu nan take.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya sanyawa hannu.

“Za a iya tunawa cewa an dakatar da kwamishinan bisa zargin lalata da matar aure da ake yi masa kan faruwar wani al’amari daga rahotan hukumar Hisbah ta jihar Kano”, inji Sakataren Gwamnatin.

Sanarwar ta ce an dage dakatarwar ne bayan kotu ta wanke Kwamishinan.

 

 

 

Kotu ta wanke Kwamishina daga jihar Jimawa bisa zargin lalata da matar aure
Sarkin Musulmi

Sarakuna ba sa tsoron gwamnoni – Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Mohammad Abubakar II, ya musanta zancen cewa sarakunan gargajiya na jin tsoron gwamnonin jihohi.

Daily trust ta rawaito cewa Sarkin ya ce sarakunan gargajiya sun fara mulki tun kafin a kafa Najeriya a shekarar 1960, yana mai cewa a matsayin sarakuna, suna da babbar rawar da suke takawa da kuma fahimtar kasa fiye da gwamnonin jihohi.

Ya bayyana hakan ne a Abuja a ranar Talata yayin wani taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan ci gaban matasan Arewacin Najeriya, wanda Gidauniyar Tunawa da Sir Ahmadu Bello ta shirya.

Sarkin gargajiyan ya kuma mayar da martani kan furucin tsohon Gwamnan Jihar Neja, Babangida Aliyu, wanda ya ce sarakunan gargajiya na jin tsoron gwamnonin jihohinsu.

A cewar Sarkin Musulmi, “Na ji ana cewa sarakunan gargajiya na tsoron gwamnoninsu. A’a, sarakunan gargajiya ba sa jin tsoron gwamnonin. Sarakuna kawai suna girmama kansu, suna girmama gwamnonin da ke da iko a jihohi daban-daban, ba wai tsoro ba.

“Duk abin da ya faru, ba ma saduda. Muna barin komai ga Allah Madaukakin Sarki, wanda yake kawo sauye-sauye a duniya, kuma muna karɓar sauye-sauyen kamar yadda suka zo.”

 

'yan bindiga
garkuwa da mutane6

 

  • Ƴan bindiga sun hallaka ƴan banga 4, a Anambra
  • Wasu ‘yan bindiga sun kashe jami’an ‘yan sanda hudu na Anambra da ƙona motoci da kuma ƴan bangaa safiyar ranar Litinin a jihar Anambra.

    An kashe uku daga cikin ‘yan banga a Ukpo da ke karamar hukumar Dunukofia a jihar yayin da aka kashe daya a Abatete, karamar hukumar Idemili ta Arewa.

    An bayyana cewa ‘yan bindigar sun afkawa Abatete, inda suka yi ta harbi ba kakkautawa, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum guda.

    Hare-haren sun faru ne biyo bayan umarnin gwamna Charles Soludo, inda ya bukaci ‘yan kasuwa da su yi watsi da umarnin zaman gida da kungiyar ‘yan asalin yankin Biafra (IPOB) ta bayar a ranar Litinin, su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum.

    Wani shaidar gani da ido ya bayyana cewa bayan kashe ‘yan AVS guda uku a Ukpo, ‘yan bindigar sun kona motar da suke aiki tare da gudu, inda suka tafi da mutane kusan bakwai tare da jikkata wasu da dama a cikin lamarin.

    Ƴan bindiga sun kashe wani manomi tare da sace wasu 6 a Taraba

    An bayyana cewa wani dan kasuwa da dan banga sun tsere da raunukan harbin bindiga.

    A cewar wanda lamarin ya faru a kan idonsa, ‘yan bindigar sun isa zagayen Ukpo, inda Da ganin wata motar bas ta Sienna tana jigilar ‘yan banga, sai suka bude wuta, inda uku daga cikin ma’aikatan suka mutu.

Wasu ‘yan bindiga sun kashe jami’an ‘yan sanda hudu na Anambra da ƙona motoci da kuma ƴan bangaa safiyar ranar Litinin a jihar Anambra.

‘Yan  bindigan sun kashe uku daga cikin ‘yan banga a Ukpo da ke karamar hukumar Dunukofia a jihar yayin da aka kashe daya a Abatete, karamar hukumar Idemili ta Arewa.

An bayyana cewa ‘yan bindigar sun afkawa Abatete, inda suka yi ta harbi ba kakkautawa, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum guda.

Hare-haren da ‘yan bindigan sun faru ne biyo bayan umarnin gwamna Charles Soludo, inda ya bukaci ‘yan kasuwa da su yi watsi da umarnin zaman gida da kungiyar ‘yan asalin yankin Biafra (IPOB) ta bayar a ranar Litinin, su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum.

Wani shaidar gani da ido ya bayyana cewa bayan kashe ‘yan AVS guda uku a Ukpo, ‘yan bindigar sun kona motar da suke aiki tare da gudu, inda suka tafi da mutane kusan bakwai tare da jikkata wasu da dama a cikin lamarin.

Ƴan bindiga sun kashe wani manomi tare da sace wasu 6 a Taraba

An bayyana cewa wani dan kasuwa da dan banga sun tsere da raunukan harbin bindiga.

A cewar wanda lamarin ya faru a kan idonsa, ‘yan bindigar sun isa zagayen Ukpo, inda suka rika harbe-harbe.

Da ganin wata motar bas ta Sienna tana jigilar ‘yan banga, sai suka bude wuta, inda uku daga cikin ma’aikatan suka mutu.

Shaidan gani da ido ya bayyana cewa, “Sun fito ne daga ko’ina, suna harbe-harbe kai-tsaye suna rera taken ‘Ba Biafra, Babu ‘Yanci.’ Mutane sun fara gudu don tsira.”

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya bayyana cewa jami’in ‘yan sanda (DPO) na Ukpo yana nan a kasa domin ya binciki lamarin.

Idan dai za a iya tunawa, makonni biyu da suka gabata, Gwamna Soludo ya umarci dukkan kasuwannin jihar da su bude tare da yin watsi da dokar zama a gida da ‘yan bindigar suka aiwatar.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button