Messi ya yi fushi da alƙalin wasa bayan tafiya hutun rabin lokaci

Spread the love

Messi ya yi fushi da alƙalin wasa bayan tafiya hutun rabin lokaci akan me yasa ba a baiwa ɗan wasan Paraguay Omar Aldarete katin kora ba, jim kaɗan bayan dawowa daga hutun rabin lokacin ɗan wasan shine ya zura ƙwallon da ta ba Paraguay nasara akan Argentina.

Wajibi ne Ghana ta cinye duka wasanninta biyu da za ta buga, ɗaya da Angola yau da kuma na gaba da Nijar kafin ta samu damar zuwa AFCON.

Tuni giwayen Afrika, Najeriya, Kamaru da Masar suka samu tikitin shiga gasar da Moroko za ta karɓi baƙuncinta a shekara mai zuwa.

Kocin Spain Luis De La Fuente ya cire Pau Cubarsí daga cikin tawagar sa.

Dan wasan baya cikin tawagar Spain da za ta kara da Denmark. De La Fuente ya cire shi

 

Komawa zuwa baya a lokacin murnar cin kwallon Bafetimbi Gomis wanda ya firgita wannan Yaron mai bada kwallo a fili a cikin 2018.

Gomis ya sanar da yin ritaya daga buga kwallo a ranar Litinin, yana da shekaru 39.

 

Wani dan kasar Paraguay ya ɗaga rigar Cristiano Ronaldo a gaban Leo Messi lokacin da ya zo yin bugan kusurwa.

 

A hukumance: Erling Haaland yanzu ya ci kwallaye (35) a raga fiye da Diego Maradona (34) a ƙasa.

 

Niger sun shammaci Sudan da ci 4-0.

Zakarun gasar nahiyar Afirka sau huɗu Ghana, an kawo ƙarshen zuwan su gasar AFCON sau 10 a jere bayan nasarar da Niger ta samu akan Sudan jiya.

Ghana na buƙatar Sudan ta yi nasara akan Niger domin ta raya fatan su na buga gasar AFCON 2025.

Kafin shiga wasan, Niger sune na ƙarshe a Rukunin ba tare da sun samu nasara ko sau ɗaya ba, ya yin da su kuma Sudan rashin nasara ɗaya kawai suka yi a wasan neman gurbin AFCON da kuma wasan neman gurbin buga gasar cin kofin duniya a 2024.

Kyamara ta gano Vinícius Jr, ya ci mutuncin mai horaswa na huɗu a cikin tawagar Venezuela a wasan da suka fafata da Brazil, cikin yaren Portugal Vinícius yace wa mai horaswar: “Vete a tomar por el c.”, Ma’ana: “w*wan banz* kawai.” SPORT ne suka rahoto.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button