An yi jana’izar Lagbaja yau a Abuja
A yau Juma’a ne aka yi biso na Hafsan Sojin kasa (COAS) Laftanar Janar Taoreed Lagbaja a Abuja, bayan shafe tsawon lokaci ya na aikin soji
A yau Juma’a ne aka yi biso na Hafsan Sojin kasa (COAS) Laftanar Janar Taoreed Lagbaja a Abuja, bayan shafe tsawon lokaci ya na aikin soji
An gudanar da jana’izar sa ne a makabartar kasa da ƙasa da ke babban birnin tarayya bayan shafe kwanaki biyu ana gudanar da zaman juyayi da aka fara a Legas a farkon makon nan.
An saukar da gawarsa da misalin karfe 4:41 na yamma tare da rakiyar jami’an tsaro, bayan an yi jana’izar a cibiyar kiristoci ta kasa da ke Abuja.
A gefe guda shugaban kasa, Bola Tinubu ya bayar da lambar yabo ta kwamandan rundunar sojin kasa ga marigayi babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja.
Ya bayyana hakan ne a lokacin bikin karrama marigayi a makabartar kasa da ke Mogadishu, Abuja. Shugaban ya yaba da kyawawan halaye na marigayi , inda ya yaba da irin gudunmawar da ya bayar ga tsaron kasa.
A cewar Tinubu, nadin Lagbaja a matsayin shugaban hafsan tsaro na daya daga cikin kwarewarsa a aikin sojin
Uwargidan marigayi Lagbaja, Mariya ita ce ta karbi lambar yabo a madadin iyalan Lagbaja cikin jinjina da girmamawa.