Gwamnatin tarayya za ta ciyo bashin dala biliyan 2.2 don tallafawa tattalin arziki
Majalisar zartaswa ta tarayya ta amince da shirin karbo rancen dala biliyan 2.2 daga ƙasar waje da nufin bunkasa kudaden kasa da tallafawa sauye-sauyen tattalin arziki da ake gudanarwa.
Ministan Kudi Wale Edun ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Alhamis bayan kammala taron majalisar, wanda shugaba Bola Tinubu ya jagoranta a fadar shugaban kasa.
A cewarsa, “Manufar farko ita ce ta kammala shirin karbo rancen waje na gwamnatin tarayya tare da amincewar kunshin tallafin dala biliyan 2.2, wanda zai hada da shiga kasuwannin babban birnin duniya ta hanyar hada-hadar Eurobonds da Sukuk bond—kimanin dalar Amurka biliyan 1.7 daga cikin kudaden. Yurobond tayin da dala miliyan 500 daga tallafin Sukuk.
Za a kammala ainihin yadda za a samar da kudaden ne da zarar Majalisar Dokoki ta kasa ta yi nazari tare da amincewa da shirin karbar bashi. Bayan an ba da izinin rancen waje, za a tara kuɗin da wuri-wuri a cikin shekara.
A farkon wannan shekarar, mun nuna yadda kasuwannin hada-hadar kudi na Najeriya ke da tsayin daka da kuma karfinsu wajen gudanar da ayyuka masu sarkakiya da nagartattun kayayyaki, kamar bayar da lamuni na dala a cikin gida wanda ya jawo masu zuba jari daga Najeriya da kasashen waje.