YANZU-YANZU: Wutar lantarkin Najeriya ta sake lalacewa
Wutar lantarki ta Najeriya ta sake lalacewa karo na goma a cikin shekarar 2024 bayan kwanakin kadan da gyarawa.
Kamfanin Rararraba wutar lantarki na kasa (TCN) ya ce wutar ta dauke ne da misalin karfe 2 na ranar Talata.
Da misalin karfe 1 na rana karfin wutar da aka samar a layin shi ne megawat 2,711, amma zuwa karfe biyu karfin wutar ya tsiyaye gaba daya.
Kawo yanzu dai TCN bai bayar da bayan musabbanin daukewar wutar gaba daya ba.