Zulum ya amince da gyaran babban asibitin garin Uba, Makarantu 8, da hanyoyin cikin gari.

Spread the love

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya amince da gyara babban asibitin Uba da kuma wasu hanyoyin garin.

Gwamnan ya kuma amince da gyara makarantun firamare guda 8 a garin Uba da suka hada da Uba Central Primary School, Mufa A Primary School, Kuma Primary School, Masil Primary School, Uba Marghi Primary School, Low-Cost Primary School, Kwarghi Primary School da Mufa B. Makarantar Firamare.

Zulum ya sanar da amincewar ne a ranar Asabar a fadar Sarkin Uba, Alhaji Ali ibn Ismaila Mamza. Hakazalika, gwamnan ya sanar da gina sabon katafaren fadar da zai dace da matsayin sarkin.

Gwamnan ya ce, Dole ne ku gudanar da gyara gaba daya, samar da kayan daki da kuma tabbatar da an tura isassun malamai.

Zulum ya kasance a yankin Kudancin Borno don tantance ayyukan da ake gudanarwa, domin daidaita aiwatar da manufofi da kuma amincewa da karin ayyuka.

Gwamnan ya ziyarci makarantar firamare ta tsakiya, sabuwar makarantar islamiyya da aka gina, da babban asibitin Uba da makarantar sakandare ta gwamnati, Uvu, inda ya tantance aikin da ake gudanarwa da kuma matakin da ake bukata domin gyarawa.

Zulum ya kuma bada umarnin gina rijiyar burtsatse mai zurfi na babbar kwalejin Islamiyya dake Uba.

Zulum ya kuma kasance a kauyen Uvu da ke karamar hukumar Askira-uba, inda ya jagoranci gina sabuwar makarantar sakandare da kuma gyara makarantar firamare ta tsakiya.

Gwamnan ya kammala ayyukan sa na ranar Asabar da ziyarar mai martaba Sarkin Askira, Alhaji Dr Albdullahi Mohammed Askirama II, ya kuma kwana a garin Askira.

A halin da ake ciki, Gwamna Babagana Umara Zulum ya kuma ba da umarnin a dauki likitoci 4 aiki a babban asibitin Uba, domin inganta ma’aikata.

Zulum ya ce, Ku yi hulɗa da CMD don ganin yadda za mu iya tura likitoci har 4 yayin da za mu yanke shawarar ko za mu gyara wannan ko kuma gina sabon asibiti.

Uba birni ne, Likitoci za su iya zuwa su zauna, kuma za mu ba su albashi. Dole ne mu tabbatar da isassun magunguna da kayan masarufi a wannan asibitin, in ji Zulum.


Spread the love

Related Articles

Back to top button