Mun rage yaran da ba su zuwa makaranta a Borno zuwa 700,000 – Zulum

Zulum: Mun rage yaran da ba su zuwa makaranta a Borno zuwa 700,000

Spread the love

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya bayyana cewa an samu raguwar yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar, lamarin da ya sa adadin ya ragu daga sama da miliyan 2.2 zuwa kasa da 700,000, wanda kashi 70% ya ragu.

Mun rage yaran da ba su zuwa makaranta a Borno zuwa 700,000 – Zulum
Gwamna Zulum

Zulum ya bayyana haka ne a lokacin kaddamar da Makarantar Sakandaren Gwamnati da ke Mairi, wani shiri da Bankin Duniya ke tallafawa, tare da Halartar Daraktan Bankin Duniya a Najeriya Dr. Ndiame Diop.

Gwamna Zulum ya ce gwamnatinsa ta zuba jari mai tsoka a fannin ilimi a cikin shekaru biyar da suka gabata, da suka hada da gina makarantu 104, gyara ajujuwa 2,931, da raba miliyoyin kayayyakin ilimi kamar littattafan motsa jiki miliyan 20, litattafan karatu miliyan 2, 15. rigar makaranta miliyan, buhunan makaranta 700,000, da sauran kayan aikin koyo.

Jaridar Daily trust ta ce Gwamnan ya kuma ce dalibai 50,000 ne suke cin gajiyar shirin ciyar da makarantun jihar a duk shekara yayin da aka samar da kekuna 10,000 don taimakawa daliban karkara shawo kan kalubalen motsi.

Ya ce don magance matsalolin ilimi na tsofaffin matasan da ba sa zuwa makaranta, jihar ta mayar da hankali kan ilimin fasaha da koyar da sana’a (TVET).

Zulum ya ce an kafa cibiyoyin sana’o’in hannu guda biyar, da makarantu biyu na mata da ‘yan mata yayin da aka sake farfado da cibiyoyin koyar da sana’o’i guda tara domin horar da masu sana’a 5,000 a duk shekara, tare da basu sana’o’in dogaro da kai da kuma rage rashin aikin yi.

Rundunar ƴansanda a Kano ta kama mutum 3 da jabun kudaden ƙasar waje

 

Rundunar Ƴansanda ta Jihar Kano ta yi holon wasu mutane uku da ake zargi da samun su da jabun kuɗaɗen ƙasar waje na kimanin Naira biliyan 129.

Da ya ke jawabi ga manema labarai, Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce kuɗaɗen sun haɗa da Dalar Amurka miliyan 3, 366, 000, sai kuma sefa miliyan 51, 970,000 sai kuma kudin Nijeriya Naira miliyan 1, 443.

Kiyawa ya ce ko a baya ma sun taba kama irin waɗannan masu lefin, inda ya kara da cewa rundunar ba za ta amince da irin wannan ta’ada ba.

Ya kuma baiyana gagarumin ci gaba wajen rage yawaitar aikata laifuka a fadin jihar, ta hanyar amfani da dabarun hadin gwiwa wanda ya hada da tsaron al’umma, ayyukan bincike na sirri, da kai farmaki kan maboyar masu aikata laifi.

Jaridar Daily Nigerian Hausa ta ruwaito cewar A cewar Kwamishinan ‘Yansanda, CP Salman-Dogo Garba, rundunar ta samu nasarar kama mutane 62 da ake zargi da aikata manyan laifuka, ciki har da fashi da makami, garkuwa da mutane, da kuma satar shanu, daga ranar 25 ga Nuwamba zuwa 9 ga Disamba, 2024.

CP Salman-Dogo Garba, wanda ya yi jawabi ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, a hedkwatar ‘yansanda da ke Bompai, Kano, ya bayyana cewa manyan nasarorin da aka samu sun hada da kama mutane takwas da ake zargi da fashi da makami, mutane goma da ake zargi da satar shanu, da kuma mutane uku da ake zargi da yin garkuwa da mutane.

An ceto mutum guda da aka yi garkuwa da shi da kuma wani mutum daya da aka sace, baya ga mutane 10 da aka ce suna karkashin cinikin mutane.

Kiyawa ya kuma bayyana cewa, idan akwai gaggawa ko bukatar kai rahoton wani abin da ake zargi, ana iya tuntuɓar rundunar ‘yan sanda ta Kano ta wadannan lambobi: 08032419754, 08123821575, da 09029292926.

Kwamishinan ‘yan sanda ya godewa Gwamnatin Jihar Kano, sauran hukumomin tsaro, da masu ruwa da tsaki a al’umma bisa goyon baya da hadin kan da suke bai wa rundunar.

Labarai masu alaƙa 

Zulum ya nemi tallafin bankin duniya don farfado da jihar Borno da rage ambaliyar ruwa 2024


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button