Zan soke auran jinsi, mu jinsi biyu kadai muka sani mace da namiji ~ Donald Trump
Zaɓaɓɓen Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ana rantsar da shi zai haramta duk wani nau’i na sauya halitta ko jinsi ko yancin zabar jinsi a duka jihohi 50 na Amurka “jinisi biyu dokar kasarmu za ta aminta dashi, namiji da mace” duk sauran zan soke su.
Shugaba Trump ya kuma ce zai dakatar da duk hukumomin ƙasar daga cigaba da biya ko tallata ayyukan jinsi.
Sannan zai umurci a rufe duk wata cibiyar kiwon lafiya dake sauya wa mutane jinsinsu. Kuma zai bada dama jama’a su kai ƙarar duk likita ko Asibitin da ya sauya masu halitta domin biyan diyya sannan ya ce zai kwace lasisin duk cibiyar lafiyar da ya kama da laifin sauya wa mutane jinsi a kasar.
Mista Trump ya kuma kara da cewa zai umurci ma’aikatar ilimi ta rushe duk wasu koyarwa da hure kunne da ake yiwa dalibai kan basu ƙwarin guiwa ta sauya halittarsu “ya kuma sha alwashin zai janye duk wasu kayan karatu dake gurbata tunanin dalibai su sauya halitta ko jinsinsu”.
“In banda rashin waye wa da rashin tunani ta yaya Gwamnatin da ta san abunda take yi za ta gurɓata tunanin matasan kasarta su rika sauya halitta ko jinsi” inji Donald Trump.