Zamuyi amfani da jirage masu saukar ungulu – hukumar kiyaye hadura ta kasa
Hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) ta bayyana shirin ta na samar da jirage masu saukar ungulu domin sintiri a dai dai lokacin da ake fara bukukuwan watan Disamba
Da yake jawabi a wajen taron watannin Ember a Abuja, Mataimakin Shugaban Rundunar, Clement Oladele ya bayyana cewa, sun jima suna shirin tun a baya,
Haka kuma ana shirin hada motocin daukar marasa lafiya da jirage marasa matuka don tallafawa ayyukan sintiri na hukumar.
Tsakanin watan Janairu zuwa Satumba na 2024, an yi asarar rayuka 3,767 a hatsarin mota 7,011, yayin da 22,373 suka samu raunuka. Hukumar ta FRSC na da burin magance hakan ta hanyar samar da ababen more rayuwa da horar da jami’anta da kuma wayar da kan direbobi, musamman kauracewa shan barasa yayin tuki.
Kofur Marshal Shehu Mohammed ya bayyana cewa hadurran kan tituna sune na bakwai da ke haddasa mace-mace a duniya kuma shine kan gaba wajen mace-macen matasan Afrika.
Domin rage haddura, gwamnati na hada kai da ma’aikatar ayyuka don gyara yanayin tituna kafin lokacin bukukuwan kirsimeti.