Za a cigaba da samun matsaloli idan aka fifita siyasa akan Tsaro
Gwamnan jihar Edo mai barin gado, Godwin Obaseki, ya shawarci gwamnan jihar mai jiran gado, Sanata Monday Okpebolo, da kada ya fifita siyasa a kan tsaro, yana mai cewa za a samu matsala idan ya yi hakan.
Obaseki ya ba da wannan shawara ne a Benin yayin taron tsaro na jihar da shugabannin hukumomin tsaro a jihar. Ya ce gwamnatinsa na barin tsaron jihar fiye da yadda ya same ta a shekarar 2016.
“Shawarata ga gwamnati mai zuwa ita ce ta dauki harkar tsaro da muhimmanci kuma kada ta ba da fifiko kan harkokin siyasa a kan tsaro domin za a samu matsaloli saboda ‘yan kasa na bukatar samar da yanayi mai tsaro.
“Mun nuna cewa mai yiwuwa ne saboda muna da maza da mata wadanda ke da kwarewa da horarwa don ba da ayyukan tsaro ga jihar da jama’ar jihar,” in ji Obaseki.