Zaɓaɓɓen gwamnan Edo ya dakatar da karɓar haraji a jihar
Sabon Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo, wanda aka rantsar da shi a jiya Talata, ya bayar da umarnin dakatar da duk wani haraji nan take ba tare da wani lokaci ba, musamman wanda ake karba a tashoshin mota har sai baba-ta-gani.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan, Fred Itua ya fitar a yau Laraba a Benin.
Okpebholo ya kuma umarci kwamishinan ‘yan sandan jihar da ya kama duk wanda ya karya dokar.
Itua ya bayyana cewa gwamnan zai duba batutuwan da suka dabaibaye harkar haraji a jihar nan ba da jimawa ba tare da yanke shawara kan sabon tsarin da za a bi.