Yau ake bikin ranar yaki da cutar ciwon siga wato diabetes ta duniya
Yayin da a yau ake bikin ranar yaki da cutar ciwon siga ta duniya ko kuma diabetes, masu fama da cutar a Najeriya na kokawa a kan yadda farashin magungunan da suke amfani da su suka yi tashin gorran zabbi.
Wani daga cikin marasa lafiyar ya ce ya kan kashe tsakanin naira dubu 80 zuwa dubu 100 kowanne wata domin sayen magungunan da yake amfani da su, sabanin watannin baya inda yake kashe tsakanin naira dubu 20 zuwa dubu 50.
Wasu daga cikin masu fama da cutar sun ce yanzu sun fi mayar da hankali a kan abinda za su ci, maimakon sayen magungunan magance cutar.
Masana kula da lafiya a kasar na danganta tsadar magungunan da faduwar darajar naira, domin akasarin magungunan daga kasashen ketare ake shigar da su cikin Najeriya.
Majalisar dinkin duniya ta ware wannan ranar ce domin ankarar da duniya illar cutar da kuma bada shawarwari akan yadda za’a tinkare ta.