YANZU-YANZU: Tinubu ya bada umurnin a saki yaran da aka kama kan zanga-zangar tsadar rayuwa.
YANZU-YANZU: Tinubu ya bada umurnin a saki yaran da aka kama kan zanga-zangar tsadar rayuwa.
Shugaba Bola Tinubu ya bada umarnin gaggauta sakin yara ƙanana da aka kama suna ɗaga tutar Rasha a zanga-zangar #EndBadGovernance da aka yi a Jihar Kano.
Ministan yaɗa labarai da wayar da kan al’umma, Mohammed Idris ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da fadar shuhaban ƙasa a ranar litinin.
Idan ba a manta ba, Gwamnatin Kano tare da rundunar yan sandan Jihar Kano ta miƙa waɗannan yara zuwa birnin tarayya bayan tattara bayanai da bincike, an tuhume su da laifin cin amanar ƙasa.