Yanzu-yanzu: Gwamnan Kano Yusuf ya kori Sakataren gwamnati, shugaban ma’aikata da kwamishinoni 5
Gwamnan Kano
Gwamnan jihar Kano Abba Yusuf ya kori sakataren gwamnatin jihar Abdullahi Bichi da Shehu Sagagi, shugaban ma’aikatan fadar sa, a wani gagarumin sauyi da ya yi a majalisar ministocinsa.
Mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature ne ya sanar da hakan yayin ganawa da manema labarai a fadar gwamnatin Kano.
Bature ya bayyana cewa, sake fasalin ya kuma shafi kwamishinoni biyar da suka hada da na kudi, ayyuka na musamman, yada labarai da harkokin cikin gida, da raya karkara da al’umma.
A cewar sanarwar, gwamna Yusuf ya ci gaba da cewa shawarar da aka dade ana jira ta zo ne domin samar da ingantaccen aiki wanda zai haifar da ribar dimokuradiyya ga al’ummar jihar Kano.
“Wadanda babban tashin hankalin ya shafa sune shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Alh. Shehu Wada Sagagi, wanda yanzu ofishinsa ya ruguje, da sakataren gwamnatin jihar, Dakta Abdullahi Baffa Bichi, wanda aka sallama bisa dalilan lafiya.
“Gwamna Yusuf ya tsige wasu daga cikin ‘yan majalisar ministocin, ya kuma sauya wa wasu ma’aikatu domin inganta ayyukan gudanar da mulki da na siyasa.
“Wadanda suka rike mukaman su ne babban lauya kuma kwamishinan shari’a, Barr. Haruna Isa Dederi; Kwamishinan Noma, Dr. Danjuma Mahmoud; Kwamishinan Lafiya, Dr. Abubakar Labaran; Kwamishinan tsare-tsare na kasa da na jiki, Hon.
Abduljabbar Mohammed Umar; Kwamishinan kasafi da tsare-tsare Hon Musa Suleiman Shannon; da Kwamishinan Ayyuka da Gidaje, Engr. Marwan Ahmad.
“Haka zalika akwai kwamishinan albarkatun kasa da ma’adinai, Sefiyanu Hamza; Kwamishinan harkokin addini, Sheikh Ahmad Tijani Auwal; Kwamishinan matasa da wasanni, Hon.
Labarai Masu Alaka
Babachir: Jihohin Arewa za suyi arziki idan aka ayyana dokar haraji akan noma–2024
Mustapha Rabiu Kwankwaso; Kwamishinan zuba jari da kasuwanci, Adamu Aliyu Kibiya; da na Tsaron Cikin Gida da Ayyuka na Musamman, Manjo Janar Mohammad Inuwa Idris Rtd.
“Wadanda aka sake nada su ne mataimakin gwamna, Kwamared Aminu Abdulssalam, wanda daga ma’aikatar kananan hukumomi zuwa manyan makarantu; Hon. Mohammad Tajo Usman, wanda aka koma daga Kimiyya da Fasaha zuwa ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu; da Dr. Yusuf Ibrahim Kofar Mata daga manyan makarantu zuwa kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire.
Jaridar VANGUARD NEWS ta rawaito cewa “Sauran da ke cikin jerin sunayen da aka tura sun hada da Hon. Amina Abdullahi, daga ayyukan agaji da rage radadin talauci zuwa ma’aikatar mata, yara da nakasassu; Hon. Nasiru Sule Garo, daga ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi zuwa ma’aikatar ayyuka na musamman.
“A cikin jerin sunayen da aka sake sanyawa akwai Hon. Ali Haruna Makoda, wanda ya tashi daga albarkatun ruwa zuwa ma’aikatar ilimi; Hon. Aisha Lawal Saji daga ma’aikatar mata, yara da nakasassu zuwa yawon bude ido da al’adu; da Hon. Muhammad Diggol daga sufuri zuwa ma’aikatar sa ido da tantance ayyukan.
“A halin da ake ciki, Gwamna Yusuf ya sauke mambobi biyar na majalisar ministocinsa da Ibrahim Jibril Fagge na ma’aikatar kudi; Ladidi Ibrahim Garko, Al’adu da yawon bude ido; Baba Halilu Dantiye, Labarai da Harkokin Cikin Gida; Shehu Aliyu Yammedi, Ayyuka na Musamman; da Abbas Sani Abbas, Ci gaban Karkara da Al’umma.
“Har ila yau, gwamnan ya umurci shugaban ma’aikata da kwamishinoni biyar da aka sallama da su kai rahoto ga ofishin gwamnan don yiwuwar sake aiki,” in ji sanarwar.
A halin da ake ciki dai, sauyin shekar majalisar na zuwa ne kasa da watanni 19 da fara aiki.