YANZU-YANZU: Gwamna Dikko ya kaddamar da sabbin jami’an tsaron cikin gida kashi na biyu domin kawo karshen matsalar tsaro a Katsina

Spread the love

Gwamnatin Jihar Katsina ta Ƙaddamar da Jami’an Tsaron Cikin Gida (Community Watch Corps) Rukuni na II

YANZU-YANZU: Gwamna Dikko ya kaddamar da sabbin jami'an tsaron cikin gida kashi na biyu domin kawo karshen matsalar tsaro a Katsina

A ranar Juma’a 8 ga watan Nuwamba 2024, Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda PhD, CON, ya ƙaddamar da Rukuni na II na jami’an tsaron cikin gida (Cwatch) guda 550 da suka fito daga kananan hukumomi goma da ke maƙwabtaka da ƙananan hukumomin da yan ta’adda suka fi addaba.

YANZU-YANZU: Gwamna Dikko ya kaddamar da sabbin jami'an tsaron cikin gida kashi na biyu domin kawo karshen matsalar tsaro a Katsina

A jawabin buɗe taron Kwamishinan tsaron cikin gida Dr. Nasir Mu’azu, ya bayyana yau muna ƙaddamar da jami’an tsaron cikin gida rukuni na biyu wannan ya biyo bayan ƙoƙarin mai girma gwamna na ganin cewa an kawo ƙarshen ta’addanci a jihar Katsina.

Jami’an tsaron kuma mun ɗauko su ne daga ƙananan hukumomi goma da suke maƙwabtaka da ƙananan hukumomin da muka ɗauko rukunin farko wanda anan ne matsalar tafi ta’azzara.

Ƙananan hukumomin da suka fito sun haɗa da Funtua, Malumfashi, Ɗanja, Bakori, Musawa, Matazu, Charanchi, Batagarawa Kurfi, da Dutsin-ma, ya kuma bayyana jami’an sun samu horo ta tare da dabarun yaƙi fiye da wanda aka baiwa na baya.

A jawabin shi gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda PhD, CON, ya bayyana wannan rana a matsayin rana mai muhimmanci a jihar Katsina da kuma tarihin wannan gwamnatin tashi, sabo da rana ce da zamu sake ƙaddamar da rukuni na biyu na jami’an tsaron cikin gida.

YANZU-YANZU: Gwamna Dikko ya kaddamar da sabbin jami'an tsaron cikin gida kashi na biyu domin kawo karshen matsalar tsaro a Katsina

Shekarar da ta gabata munyi nasarar samun sa’a a cikin wannan yaƙin da muke da yan fashin daji duba da yanda wancen rukunin na jami’an mu haɗin guiwa da jami’an tsaro suka daƙile hare-hare da dama a faɗin jihar Katsina, wanda hakan yaba manoman mu damar yin aikin gona cikin kwanciyar hankali sabo da kaso chasa’in da biyar na gonakin Katsina an noma su a bana.

Duk a cikin hanyoyin da muke bi wajen daƙile matsalar nan mun samar da alawus ga sama da mutum 6,000 da suka haɗa da masu unguwanni, limamai, da kuma ladanai, domin sune ke cikin al’umma kuma sune zasu iya taimakawa jami’an tsaron namu wajen gudanar da ayyukan su ta hanyar shawarwari da kuma bayanan sirri.

YANZU-YANZU: Gwamna Dikko ya kaddamar da sabbin jami'an tsaron cikin gida kashi na biyu domin kawo karshen matsalar tsaro a Katsina

Daga ƙarshe ina kira gare ku da ku nuna halin ɗa’a a lokacin gudanar da ayyukan ku kuma kuyi aiki tuƙuru domin ganin mun ceto jihar mu daga wannan hali da take ciki kuma kowanen ku ba zai tafi gida ba tare da ya amshi dukkan wasu kayan aiki da suka dace ba ga Babura da motocin da muka tanadar maku nan.

Insha Allah kuma ina da tabbacin zamu kawo ƙarshen wannan matsalar a jihar Katsina.

Wanda suka halarci wurin akwai Mataimakin gwamnan jihar Katsina Hon. Faruk Lawal Joɓe, Kakakin majalisar dokokin jihar Katsina Rt.Hon Nasiru Yahya Daura, Shugaban ma’aikatan gidan gwamnati Hon. Jabiru Abdullahi Tsauri, Sakataren Gwamnan Hon. Abdullahi Aliyu Turaji, yan majalisar Dokoki, yan majalisar zartarwa da sauran su.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button