Yankin Lagos na yunƙurin mallake Arewacin Nijeriya: Kwankwaso

Sanata Rabiu Kwankwaso ya zargi gwamnatin Tarayyar Nijeriya da ƙoƙarin durƙusar da harkokin kasuwanci a Arewacin ƙasar ta hanyar fito da sabuwar dokar haraji.

Spread the love

Tsohon gwamnan Kano kuma ɗan takarar shugaban Nijeriya na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi zargin cewa yankin Lagos yana yunƙuri “mai ƙarfi na mallake” Arewacin Nijeriya.

 

Jagoran na jam’iyyar NNPP, ya yi wannan zargi ne a Kano ranar Lahadi lokacin bikin yaye ɗaliban Jami’ar Skyline da ke birnin na Kano.

 

Duk da yake bai ambaci sunayen mutanen yankin na Lagos da yake zargi suna neman yi wa Arewacin ƙasar mulkin mallaka ba, sai dai wasu na gani yana magana ne game da shugaban Nijeriya Bola Tinubu wanda tsohon gwamnan Lagos ne kuma babban mai faɗa a ji a yankin Kudu Maso Yammacin Nijeriya.

 

Kwankwaso ya ce: “Akwai yunƙuri mai ƙarfi daga Yankin Lagos na mallake wannan ɓangare [ Arewaci] na Nijeriya.”

 

Kwankwaso ya gargadi ma’aurata su guji duba wayoyin juna

 

Tsohon gwamnan na jihar Kano ya ce hakan ne ya sa wasu mutanen yankin na Lagos suka tsoma baki a harkokin masarautar jihar Kano inda suka hana gwamnatin jihar zaɓen sarkinta.

 

“A yanzu, Lagos ta hana mu zaɓen Sarkinmu shi ya sa Lagos ta shigo har tsakiyar Kano ta saka nata sarkin,” in ji Kwankwaso.

 

Kazalika jagoran na jam’iyyar NNPP ya zargi gwamnatin tarayyar Nijeriya da yunƙurin durƙusar da harkokin kasuwanci a arewacin ƙasar ta hanyar fito da sabuwar dokar haraji.

 

Kawo yanzu dai babu wani martani a hukumance game da wannan zargi.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button