‘Yan ta’addan Lakurawa sun tsere a Kebbi yayin da sojoji suka kai musu hari a maboyarsu

Spread the love

‘Yan kungiyar da ke dauke da makamai na Lakurawa sun yi ta ja da baya a yayin da sojoji ke kai hare-hare ta kasa da sama a kan sansanonin kungiyar a fadin jihohin Kebbi da Sokoto.

Bayan wani hari da kungiyar Lakurawa ta kai kan al’ummar Mera a karamar hukumar Augie a jihar Kebbi, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 17, hedkwatar sojojin ta aike da tawagar sojoji zuwa yankin.

Da isar sojojin a Birnin Kebbi, a cewar Abdullahi Idris Zuru, mai taimaka wa gwamnan Kebbi kan harkokin yada labarai, sun gana da mataimakin gwamna Abubakar Umar Tafida a ofishin majalisar zartarwa kafin su wuce zuwa Mera.

Zuru ya ce sojojin sun yi nasarar fatattakar ‘yan ta’addan tare da kwato shanu da dama da suka bari a baya yayin da maharan suka gudu.

Wannan aika aika ya zo ne bayan da gwamnan jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ba da tallafin gaggawa domin magance yawaitar tashe-tashen hankulan da kungiyoyi masu dauke da makamai ke kawo cikas ga rayuwa a yankunan karkara.

Gwamnan ya yi alkawarin kare rayuka da dukiyoyin daukacin ‘yan jihar Kebbi, wanda hakan ya sa ya nemi gwamnatin tarayya ta shiga tsakani domin yakar ta’addanci a fadin jihar,” inji Zuru.

A halin da ake ciki, mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, ya bada tabbacin cewa za a fatattaki ‘yan kungiyar Lakurawa dake ta’addanci a jihohin Arewa maso Yamma daga Najeriya.

Ribadu ya bayar da wannan tabbacin ne a ranar Larabar da ta gabata a Abuja a wajen bukin bude babban taron kwastam na shekarar 2024, inda ya wakilci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Zamu fatattaki wadanda ake kira Lukarawa daga kasarmu. Za mu kunyata masu suka, mu rufe bakunansu nan da nan.

Boko Haram da suka addabi kasarmu, yanzu sun fara gudu.

Membobin kungiyar a yanzu suna tafiya zuwa wasu kasashe makwabta saboda Najeriya ba ta da amfani wajen gudanar da ayyukansu, in ji shi.

Ya kuma ce alamun da ke nuna cewa al’amura na kara inganta ta fuskar tattalin arziki wanda kowa zai iya gani, inda ya ba da misali da karuwar hako danyen mai a yankin Neja-Delta da kuma sauye-sauyen kasafin kudi da babban bankin Najeriya (CBN) ke yi a matsayin wani bangare na irin wannan kokarin.

Yawan danyen mai ya kai bpd miliyan 1.8 sannan kuma an tsaftace babban bankin kasar babu wanda ke karbar kobo daga CBN. Ya kara da cewa lokacin da muka yi alkawarin cewa za mu gyara kasar nan, za mu yi hakan ne domin Shugaba Tinubu bai taba gazawa ba.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button