‘Yan siyasar Isra’ila sun yi tir da matakin firaministan kasar Netanyahu

Spread the love

Jagoran ‘yan adawa kuma shugaban Yesh Atid Yair Lapid ya ce bai ka ma ta a kori Gallant ba a dai dai lokacin da kasar ke cikin yaki.

Shugaban jam’iyyar Democrat ta Isra’ila Yair Golan ya soki matakin da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya dauka na korar ministan tsaro Yoav Gallant, inda ya maye gurbinsa da tsohon babban jami’in diflomasiyyar Isra’ila Katz.

Daruruwan Isra’ilawa ne suka yi zanga-zanga a Tel Aviv a yammacin ranar Talata domin nuna adawa da korar Gallant, kamar yadda kafar dillacin labarai ta AFP ta ruwaito.

A wata sanarwa da ofishin Netanyahu ya fitar a baya ya ce, “A cikin ‘yan watannin da suka gabata … amana ta zube. A kan haka ne na yanke shawarar kawo karshen wa’adin ministan tsaro a yau.”

An nada Gideon Sa’ar don maye gurbin Katz a matsayin ministan harkokin waje.

Bayan sallamarsa, Gallant ya buga a kan X/Twitter cewa tsaron Isra’ila zai sanya a gaba har karshen rayuwar sa.

Shi ma shugaban kungiyar hadin kan kasa ta Isra’ila Benny Gantz ya mayar da martani inda ya ke cewar, “an sa ka siyasa a cikin tsaron kasar.”

Da yake jawabi shugaban yan adawa Yesh Atid yace “Netanyahu yana sadaukar da jami’an tsaron Isra’ila da sojojin IDF saboda rashin iya siyasa. ya kuma zargi Gwamnati da cewa ta fifita daftarin doka fiye da wadanda ke aiki,” in ji shi.

Yesh yayi kira ga mambobin sa na kungiyar Yesh Atid da dukkan ‘yan kishin kasa da su fito kan tituna a daren yau.”


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button