‘Yan sanda sun kama karnuka 3 bisa zargin su da hallaka maigadi
Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta tabbatar da kama wasu karnuka uku da ake zargin sun hallaka wani mai gadi a unguwar Pinnock Estate da ke Ilasan a yankin Lekki na jihar.
‘Yan sandan sun kuma kame mamallakin karnukan mai suna Salisu Mustapha.
Kafar yada labarai ta DCL tace Jami’an na yan sanda sun kuma bayyana cewa karnukan suna samun kyakkyawar kulawa a wajen su domin kaucewa tauye hakkin dabbobi.
Likitoci dai na bada shawari ga masu kiwon karnuka da su killace a kebebben waje domin kare al’umma daga cizon su