‘Yan majalisa sun gayyaci ministoci kan badakalar sama da dala biliyan 2.
Ministocin noma da samar da abinci, Abubakar Kyari, da takwaransa na kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire, Uche Nnaji, da na kasafin kudi da tsare-tsare, Atiku Bagudu, na daga cikin manyan jami’an gwamnati da ake sa ran za su gurfana a gaban kwamitin majalisar wakilai ranar Laraba.
Kwamitin wanda mamba mai wakiltar mazabar Ogbaru na jihar Anambra, Afam Ogene ya jagoranta yana binciken yadda aka kashe sama da dala biliyan biyu domin bunkasa hanyoyin samar da makamashi a Najeriya daga shekarar 2015 zuwa yau.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Kwamitin a makon da ya gabata ya ce duk da dimbin tallafi da jarin da ake samu a fannin, wutar lantarki na ci gaba da tabarbarewa a kasar.
A wani taro da kwamitin yayi Wanda aka shirya a ranakun Talata da Laraba, 5 da 6 ga Nuwamba, 2024, sauraron binciken ya biyo bayan umarnin da aka bai wa Kwamitin a ranar 6 ga Yuni, 2024, don bincikar Ma’aikatu da Hukumomin da ke da hannu a saka hannun jari, saye, da kuma karbar tallafi na bangaren makamashi.
A zaman majalisa da aka fara a ranar Talata, babu daya daga cikin ministocin da ya zo, inda suka aike da wakilai.
Da yake bayyana rashin jin dadinsa, Ogene ya bukaci ministocin da abin ya shafa da sauran jami’an gwamnati da su bayyana a gaban kwamitin a ranar Laraba.
Dan majalisa na jam’iyyar Labour ne ya tunatar da wakilan minstocin da aka gayyata cewa ikon kiran jami’an gwamnati domin gudanar da bincike ya rataya ne a kan majalisun dokokin kasar biyu.
Ya kara da cewa wannan ikon ya hada da binciken al’amuran duk wani mutum, hukuma, ko ma’aikatar gwamnati da aka dorawa alhakinsa
Haka kuma ana sa ran a zaman binciken da za a yi a ranar Larabar nan, akwai Ministan Albarkatun Man Fetur (Gas), Ekperikpe Ekpo, Ofishin Akanta Janar na Tarayya, Bankin Tarayyar Najeriya, Kamfanin Neja Delta Power Holding Company da Bankin Union.