Yan bindiga sun hallaka manoma 10 da Indiyawa a jihar Neja
‘Yan bindiga sun hallaka akalla manoma 10 da suka hada da mata daga kauyukan Wayam da Belu-Belu da ke karamar hukumar Rafi a jihar Neja, inda mazauna yankin suka ce an cire kawunan mutane shida daga cikin wadanda aka kashen.
Harin wanda ya auku da safiyar ranar Talata a daidai lokacin da mutanen kauyen ke gudanar da sallar asuba, ya yi sanadin jikkatar da dama, inda wasu da dama ke karbar magani sakamakon harbin bindiga a wani asibitin yankin.
Shaidu sun bayyana cewa maharan sun kuma yi garkuwa da wasu mutanen kauyukan tare da tilastawa mazauna garin Wayam, Belu-Belu, Madaka, da kewaye su gudu zuwa garin Kagara, hedikwatar karamar hukumar Rafi. Bala Tukur, wani mazaunin yankin, ya bayyana irin barnar da aka samu da kuma kawo cikas ga aikin da manoman keyi na girbe amfanin gonarsu, inda aka tilastawa da yawa barin amfanin gonakinsu, yayin da hare-haren ‘yan bindiga ke kara tsananta a yankin. A Kukoki, an ruwaito cewa manoma sun biya Naira miliyan 1.5 don kare gonakinsu, sai bayan kwanaki da ‘yan fashi suka dawo.
An samu karin kai hare-hare a fadin yankin, ciki har da wani hari da ‘yan bindiga suka kai a garin Zungeru da ke karamar hukumar Wushishi, inda aka yi garkuwa da mutanen daga gidajensu da otal-otal. Daga cikin wadanda aka sace akwai Saidu Yakubu ma’aikacin kamfanin Sino-Hydro da matarsa. Bugu da kari, an yi garkuwa da wasu ‘yan kasar Indiya biyu daga wata gonar shinkafa a Swashi, karamar hukumar Borgu, a ranar 2 ga Nuwamba, inda aka kashe wani mai gadi a yayin harin.
Gwamnatin jihar Neja wanda kwamishinan tsaro na cikin gida Birgediya Bello Abdullahi Mohammed ya wakilta, ya tabbatar da faruwar lamarin . Ya kuma tabbatar wa da mazauna yankin cewa jami’an tsaro sun shirya tsaf domin magance tashe-tashen hankula da kuma hana ci gaba da kai hare-hare a yankunan da lamarin ya shafa.
One Comment