Yadda majalisar dokoki a jihar Zamfara ta dakatar da ƴaƴanta na tsawon shekara 1 daga aiki
Ana ci gaba da samun rashin fahimta game da batun mayar da wasu ƴan majalisar dokokin jihar Zamfara kan kujerunsu, bayan da majalisar ta dakatar da su kusan shekara guda da ta gabata.
Ana ci gaba da samun rashin fahimta game da batun mayar da wasu ƴan majalisar dokoki na jihar Zamfara kan kujerunsu, bayan da majalisar ta dakatar da su kusan shekara guda da ta gabata.
Yanzu haka wasu daga cikinsu ma sun fara tunanin sauka daga mukamin na su, don a sake gudanar da zaben cike gurbi a yankunan mu ta yadda jama’arsu za su samu wakilci tun da duk wani kokari na ganin an warware matsalar bai kai ga gaci ba. Cewar majalisar dokoki.
BBC Hausa ta ruwaito cewa a ranar 27 ga watan Fabrairu ne majalisar dokoki na jihar ta Zamfara ta dakatar da wadannan yan majalisa 8 bisa zarginsu da gudanar da zaman majalisar dokoki ba bisa ka’ida ba.
Ƴan majalisar dokoki na Zamfara takwas su ne Bashir Aliyu (PDP-Gummi 1) Amiru Keta (PDP-Tsafe Ta Yamma) Nasiru Abdullahi (PDP-Maru Ta Kudu) Bashir Masama (PDP-Bukkuyum Ta Arewa) Faruku Dosara (APC-Maradun 1) Ibrahim Tukur (Mazabar APC-Bakura) Shamsudeen Hassan (APC Talata-Mafara Ta Arewa) da kuma Bashiru Sarkin-Zango (PDP-Bungudu Ta Yamma). Majalisar dokoki.
Ɗaya daga cikinsu Honarabul Ibrahim Tudu Tukur, ya faɗawa BBC Hausa cewa ”Matsalolin tsaro ne da suka ta’azzara ne suka sa muka je muka buɗe majalisa muka zauna muka yi kira ga gwamnatin jiha da ta tarayya da su dauki matakin gaggawa don magance wannan matsala, wannan shine abun da ya ɓata masu rai”. Majalisar dokoki.
Ya ƙara da cewa majalisar malamai da majalisar masarautu da shi kansa shugaban PDP na jihar da wasu jagorori kamar tsohon gwamnan jihar Abdulaziz Yari sun yi kokarin sasanta lamarin, amma dukka basu yi nasara ba. Majalisar dokoki.
To sai dai a nasa martanin mai magana da yawun majalisar dokoki na jihar ta Zamfara Hamisu Alhaji Faro, ya ce suma suna na su kokarin domin ganin an sasanta wannan al’amari, amma abun da ke kawo cikas shine su ƴan majalisar dokoki wanda aka dakatar sun ki amincewa abun da suka yi kuskure ne ballantana su ba da hakuri a yafe masu.
”Sun karya dokoki na kundin tsarin mulki, suma sun san haka, kuma an gaya masu muna so a yafewa juna, amma su zo su ba wa shugabanni hakuri musamman shi kakakin majalisa, amma suka ce Wallahi tallahi baza su yi hakan ba”
Wasu daga cikin yan majalisar dokoki na jihar da aka dakatar dai na zargin gwamnan jihar Dauda Lawal da hannu a dakatar da su kasancewarsu yan jam’iyyar APC ne, sai dai kuma a cikinsu akwai hatta ƴan jam’iyyar gwamnan ta PDP.
Wannan al’amari dai ya sa kananan hukumomin yan majalisar sun rasa wakilci a majalisar dokoki na jihar tsawon shekara guda, wani abu da ya sa masu sharhi ke ganin zai haifarwa mazaɓun na su gagarumar asara, saboda rashin waklcin da zai rika kai kokensu gaba.
Fulawa da dabbobin fadar Shugaban Ƙasa za su ci naira miliyan 125 a 2025
Za a sayi tayoyin Naira miliyan 165 da kayayyakin motsa jiki na Naira miliyan 101 a Fadar Shugaban Ƙasa a kasafin 2025
Shugaba Tinubu ya ware Naira miliyan 125 domin kula da fulawa da dabbobin Fadar Shugaban Ƙasa a shekarar 2025.
Shugaban ƙasar ya ware Naira miliyan 86 domin kula da dabbobi da kuma Naira miliyan 38.5 na kula da ciyayi da fulawar fadar ta Aso Rock a shekarar.
Kazalika an ware Naira miliyan 165 domin sayen tayoyi masu sulke, baya ga Naira biliyan 4.7 na sayen sababbin motoci.
Kayayyakin motsa jikin Fadar Shugaban Ƙasa za su ci Naira miliyan 101, a yayin da aka ware Naira miliyan 73 domin sayen na’urorin sadarwa.
Waɗannan na daga cikin abubuwan da aka ware wa Naira biliyan 47 domin kula da Fadar Shugaban Ƙasa a Kasafin na 2025.
Daga ciki akwai kasafin Naira biliyan 5.5 da aka ware domin aikin kwaskwariman fadar, sai gyaran na’urorin laturoni da sauransu da zai ci Naira biliyan shida.
Naira biliyan 1.8 kuma an ware su ne domin ƙarasa aikin gina ofisoshin masu ba da shawara a fadar shugaban ƙasa.
An kuna ware Naira biliyan 12 domin biyan bashin ayyukan gyara da kamfanin Julius Berger ya yi a Fadar Shugaban Ƙasa.
A ranar Laraba ne dai Shugaba Tinubu ya gabatar da kasafin 2025 na Naira tiriliyan 49, wanda tuni Majalisar Dattawa ta kammal karatu na biyu a kansa.
A halin yanzu kasafin na gaban kwamitin majalisar domin fara aiki a kansa.
Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya yabawa hukumar alhazai ta jihar bisa jajircewa a aikin hajji na 2024
Gwamna Uba Sani ya yabawa hukumar jin dadin alhazai ta Jihar Kaduna bisa kyakkyawan aikin da ta yi a lokacin aikin Hajjin 2024 wanda ya sa ta samu yabo a fadin duniya.
A wata sanarwa da Barista Tahir Umar Tahir, Darakta janar na hukumar hadin kan addinai ya fitar a ranar Laraba, ta ce Gwamnan ya yi wannan yabon ne lokacin da Hukumar ta mika rahoton aikin Hajjin 2024 a ranar Litinin.
Sanarwar ta ce, Gwamnan ya yi nuni da cewa Hukumar Alhazai ta kammala kwashe dukkan maniyyata zuwa Makkah, kwanaki goma kafin rufe filin jirgin sama na Sarki Abdul Azeez, wanda ya bayyana hakan a matsayin abunda ba a taba ganin irinsa ba.
Babban daraktan ya tunatar da cewa dukkan alhazan jihar Kaduna sun sauka ne kai tsaye a Madina, sun shafe kwanaki hudu a birnin, sun ziyarci wurare masu tsarki da kuma wuraren tarihi, kafin su wuce Makkah.
Barista Tahir ya kuma yi nuni da cewa mahajjatan sun shafe kusan mako guda a Makkah kafin su je Muna, inda daga nan suka wuce zuwa Arafat, inda ya kara da cewa ‘’Mai girma Gwamna Uba Sani ya yi farin ciki da wannan aiki maras kyau.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, an ba wa alhazan jihar Kaduna masauki ne ta hanyar tattaki zuwa Masallacin Harami da ke birnin Makkah, inda ta ce mahajjata sun samu mafi kyawun ciniki a kowane wurin kwanciya.
Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta yi amfani da tsarin farashin farashi na hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kaduna kuma hakan ya cancanci a yaba masa.
Saboda yadda hukumar ta zabi masauki a Makkah, a bayyane ya sa aka zabi mai kula da alhazai a matsayin mamba a kwamitin kula da gidajen kwana da masu samar da abinci na hukumar a NAHCON, inji Gwamnan.
A nasa bangaren, Shugaban Hukumar, Malam Salihu S. Abubakar, ya yaba wa Gwamna Uba Sani bisa yadda ya ba su damar gudanar da aikin Hajji.
Malam Salihu ya ci gaba da cewa, Gwamnan ya kuma baiwa hukumar tallafin da ya kamata a duk lokacin da take bukatar taimako, inda ya ce hakan yasa a shekarar 2024 ta samu nasara.
A cewar sanarwar, Malam Salihu ya samu rakiyar wasu mambobin hukumar da suka hada da Malam Baba Ahmed Rufa’i (Sakataren), da AVM Mohammed Rabiu Dabo (rtd).
Sauran mambobin kwamitin da suka halarci taron sun hada da, Malam Kasim Aminu, Imam Buhari da Ummulkulthum Mai Gwari da Malama Maimuna Waziri da Farfesa M.M Gwadabe.