Ya kama ta Tinubu ya kawo karshen wahalar da yan kasa ke ciki – Osinbajo
Tsohon mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya kara ba da muhimmanci wajen rage wahalhalun da ‘yan Najeriya ke fama da su na tattalin arziki, inda ya bukace shi da ya ba da fifita bukatun yan kasa akan komai
Osinbajo ya yi wannan kira ne a yayin taron Mata a harkan kasuwanci na shekarar 2024 inda ya bayyana mahimmancin buƙatar aiwatar da ingantaccen shirye-shiryen da za su dace da jin daɗin rayuwar jama’a da kuma samar da kiwon lafiya mai inganci, musamman yadda ‘yan ƙasa ke kokawa da hauhawar farashin kayayyaki na yau da kunlun kamar abinci, sufuri, da sauransu.
Osinbajo ya kuma jaddada matsalar karatun boko da ya addabi yankin arewacin Najeriya, inda sama da kashi 67% na mata ke fama da rashin ilimi, wanda hakan ke haifar da cikas ga ci gaban zamantakewa da tattalin arziki.
Taron ya mayar da hankali kan karfafawa mata gwiwa a harkokin gudanarwa, kasuwanci, don bunkasa hada-hadar tattalin arziki da walwalar jama’a.