Xi Jinping ya ce zai yi aiki da Donald Trump

Spread the love

Shugaban China Xi Jinping ya ce zai yi aiki tare da shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump, a wata ganawa ta karshe da ya yi da Joe Biden a matsayin shugaban Amurka.

Shugabannin biyu sun gana ne a gefen taron APEC na kasashen yankin Asia da Pacific da aka gudanar a Lima babban birnin Peru, duk da rikicin kasuwanci da sabanin ra’ayi kan rikicin Taiwan da Rasha da ke tsakanin kasashen biyu.

A ganawarsa da ta kasance ta karshe a matsayin shugaban Amurka tsakaninsa da Xi jinping, Mr Biden ya bukaci China ta yi amfani da tasirinta domin hana Rasha shigar da sojojin Koriya ta arewa yakin Ukraine.

Mr Biden ya kuma bayyana damuwarsa kan ayyukan China a kusa da Taiwan, wanda ya kira mai tayar da hankali.

Mr Xi ya ce duk da akwai tsama tsakanin Amurka da China amma a cewarsa sun taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya a duniya. Ya kuma ce huldar China da Amurka ba za ta sauya ba

Sai dai duk Mr Xi ya yi alkawalin zai yi aiki da Donald Trump, sai dai Masu sharhi sun ce dangantakar Amurka da China na iya yin tsami sosai idan Trump ya koma kan karagar mulki nan da wata biyu, sakamakon wasu dalilai da suka hada da alkawarin kara haraji kan kayayyakin da China ke shiga da su Amurka.

Trump ya yi alkawalin zai kara haraji kashi 60 na kayayyakin da China ke shiga da su Amurka.

Donald Trump dai ya ɗauki China a matsayin babbar mai hamayyar kasuwanci da Amurka, kuma dangantaka tsakanin ƙasashen biyu ta ƙara tsami a zamanin mulkin shugaban na farko inda ya kira cutar korona a matsayin wata annobar China.

Karo na uku kenan da shugaba Biden ke ganawa da takwaransa na China, da suka hada da taron APEC a bara a San Francisco inda shugabannin biyu suka amince su yaki da safarar miyagun kwayoyi da kuma sauyin yanayi.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button