Wuta Tsakar Dare Ta Tashi Shaguna A Kasuwar Kano

Wata gobara da ta tashi da sanyin safiyar yau ta kone shaguna hudu a kasuwar ‘yan Katako da ke karamar hukumar Nassarawa a jihar Kano.

Spread the love

Lamarin dai a cewar hukumar kashe gobara ta jihar Kano, ya faru ne da misalin karfe 1:51 na safe. ran juma’a.

Kakakin hukumar kashe gobara Saminu Abdullahi ya ce an samu kiran agajin gaggawa daga ASP U.I. Bushira na sashin ‘yan sanda na Dakata bisa barkewar gobarar.

Abdullahi ya bayyana cewa ma’aikatan da suka kai daukin daga tashar kashe gobara ta Bompai sun isa wurin da misalin karfe 1:56 na safe, inda suka tarar da shaguna biyu a cikin kasuwar da gobara ta cinye, “kuma da kokarin mutanenmu sun yi nasarar shawo kan lamarin.

Sai dai ya ce gobara ta biyu ta tashi a wuri guda, inda ta kone wasu shaguna guda biyu.

Abdullahi ya alakanta musabbabin tashin gobarar da matsalar wutar lantarki.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button