Wata gobara ta tashi a kasuwar kayayyakin gyara a jihar Legas
Wata gobara ta tashi a kasuwa a jihar legas
Wata gobara da ta tashi a wata kasuwar kayan gyara da ke unguwar Idumota a jihar Legas ta kuma lalata kadarori na miliyoyin naira.
A wata sanarwa da ya fitar a yau, babban sakataren hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Legas, Olufemi , ya ce gobarar ta faru ne a daren ranar Juma’a.
Olufemi ya ce binciken farko ya nuna cewa gine-gine da shagunan sayar da kayayyakin gyaran mota da dama sun kone.
Har yanzu dai ba a gano musabbabin tashin gobarar ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton
Daily trust ta ce Oke-Osanyintolu ya kara da cewa ba a samu asarar rai ba a wurin da lamarin ya faru, kuma ba a samu wani rauni ba sakamakon lamarin.
A cewarsa, ana ci gaba da kokarin kashe gobarar gaba daya.
Shaguna 11 sun kone bayan fashewar wani gas a Legas da ya haddasa gobara
Shaguna 11 ne suka kone kurmus yayin da dukiyoyi na miliyoyin Naira suka lalace a wata gobara da ta tashi a ranar Talata a kasuwar iyaka da ke unguwar Ajegunle a jihar Legas.
Babban Sakatare na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Legas, Olufemi Oke-Osanyintolu, ya ce gobarar ta tashi ne sakamakon fashewar wani abu da ya samo asali daga wani shagon sayar da kayayyaki inda aka ajiye tulun iskar gas masu girma dabam dabam.
Ya bayyana a cikin wata sanarwa a ranar Talata cewa ma’aikatan hukumar sun iya shawo kan gobarar tare da hana ta yaduwa zuwa wasu gine-ginen da ke makwabtaka da su.
Wuta Tsakar Dare Ta Tashi Shaguna A Kasuwar Kano
Jaridar Punch ta ruwaito cewar Sanarwar ta kara da cewa, “Saboda amsa kiraye-kirayen wahala ta lambobin Gaggawa Kyauta na 767/112 da karfe 9:20 na safe, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Legas ta kaddamar da Tawagar ta Response daga Onipanu Base.
Bayan isar tawagar Response ta Eagle a wurin da lamarin ya faru da misalin karfe 9:37 na dare, an ga yadda gobara ta cinye wasu shaguna a kasuwar Alayabiagba.
“Bincike da aka gudanar ya nuna cewa fashewar ta samo asali ne daga wani shagon sayar da iskar gas inda ake ajiye tulun iskar gas masu girma dabam, sakamakon yabo daga daya daga cikin silinda kafin ya bazu zuwa wasu shaguna da ke wurin da aka ambata.
Yunkurin hadin gwiwa da tawagar kuyanga da ‘yan kwana-kwana a wurin da lamarin ya faru, sun dakile gobarar tare da hana ta yaduwa zuwa wasu gine-ginen da ke makwabtaka da su.”
Gobara ta lashe kasuwar Jos jihar Filato
Wata gobara ta lalata kadarori na miliyoyin naira a kasuwar Laranto da ke karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar Filato.
Daily trust ta ruwaito cewa an sha samun barkewar gobara a kasuwar. A shekarar da ta gabata wani sashe na kasuwar ya kone kurmus sakamakon matsalar wutar lantarki, lamarin da ya yi sanadiyar lalata kayayyaki da suka hada da ababan hawa.
Wakilinmu ya tattaro cewa sabon lamarin ya faru ne da misalin karfe 11 na daren ranar Lahadi bayan da aka rufe harkokin kasuwanci a ranar.
An tattaro cewa mutane sun garzaya kasuwa da daddare domin taimakawa wajen kashe gobarar.
Shugaban kasuwar Alhaji Idris Shehu ya shaida wa Aminiya cewa gobarar ta lakume kayyakin miliyoyin naira, inda ya ce har yanzu ba a san musabbabin faruwar lamarin ba.
Ya ce, “Kusan sassa uku na kasuwar da suka hada da katako, kayan sawa na hannu da kuma kayan daki sun sami matsala sosai. Duk da cewa ba za mu iya tantance ainihin adadin kudaden da aka yi asarar ba a halin yanzu, amma tsananin barnar na nuni da cewa mun yi asarar miliyoyin naira.”
Da yake tsokaci kan lamarin, shugaban sashen katako na kasuwar, Umar Aliyu, ya koka da cewa da a ce jami’an kashe gobara sun isa kan lokaci, da an rage asarar da ake yi.
Ya ce, “Ba da jimawa ba da aka sanar da mu lamarin, mun ziyarci ofishin kashe gobara na garin, muka kai rahoton lamarin. Sai dai jami’an ofishin sun koka da cewa basu da man dizal da zai iya sarrafa motocinsu.
“Duk da kokarin da muka yi na shawo kan su, sun ki amsa, saboda karancin man dizal. Sai da Shugaban Jos ta Arewa da Kwamishinan Albarkatun Ruwa suka je suka kirawo ma’aikatan kashe gobara daga gidan gwamnati, inda a karshe suka kashe gobarar. Idan ba don tsoma bakinsu ba, da lamarin ya fi muni,” ya kara da cewa.
One Comment