Wani harin bata gari ya katse hasken lantarki a wasu yankunan Lokoja da Abuja

Spread the love

Babban Kamfanin Samar da  Lantarki na Najeriya wato TCN ya sanar da wani sabon hari da aka kai kan wasu manyan turakun da ke kan layin kai wutar lantarki  yankin Lokoja da Gwagwalada.

Sanarwar da kamfanin ya fitar, ta bayyana cewa, ta’adin da aka yi wa turakun ya haifar da babban cikas ga aikin samar da wuta a yankuna da dama na jihar Kogi da yankin Gwagwalada da ke Abuja babban birnin kasar.

A baya-bayan nan ne yankin arewacin Najeriya ya kwashe akalla kwanaki 10 ba tare da samun wutar lantarki ba, sakamakon katsewar wutar da aka gani.

Wannan ya janyo wa ‘yan kasuwa da dama asarar kayayyaki da kuma makudan kudade, musamman masu sana’ar sayen da danyen kifi da kuma dangogin nama, hadi da kayayyakin sanyi.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button