Ahmad Lawan ya bada tallafin N10m ga wadanda gobara ta shafa a jihar Yobe 

An raba tallafi ga wadan da gobara ta shafa a jihar Yobe

Spread the love

Shugaban majalisar dattawa ta 9, Sanata Ahmad Lawan, ya bayar da gudunmawar Naira miliyan 10 don tallafawa wadanda gobarar da ta barke a kasuwar bayan Tasha ta jihar Yobe a kwanakin baya.

Ahmad Lawan ya bada tallafin N10m ga wadanda gobara ta shafa a jihar Yobe 
Yobe: Ahmad Lawan

Gobarar wacce ta auku a ranar Talatar da ta gabata, ta lalata shaguna 46, ta kuma shafi sama da mutane 200 a Damaturu, babban birnin jihar.

Jaridar Daily trust ta ruwaito cewar Tawagar karkashin jagorancin mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Yobe, Y’au Usman Dachia, ta tantance barnar da aka yi kafin mika tallafin.

Sanata Lawan wanda tsohon shugaban kungiyar ‘yan kasuwar hadaddiyar kasuwa, Alhaji Nasir Mato ya wakilta, ya bayyana alhininsa game da wannan mummunan al’amari da ya faru, inda ya yi la’akari da tsananin zafi da wahala.

Ya bukaci mazauna yankin da su hada kai wajen tallafawa wadanda abin ya shafa, ya kuma yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su ba da agaji cikin gaggawa.

Da yake karbar tallafin, shugaban ‘yan kasuwar Yobe, Alhaji Muktar Kime, ya gode wa tsohon shugaban majalisar dattawan bisa yadda ya shiga tsakani a kan lokaci, yana mai jaddada matukar bukatar irin wannan tallafi yayin da ‘yan kasuwa ke kokarin kwato musu rayuwarsu.

Cibiyar kare hakkin jama’a ta ta kai karar hukumar ‘yan sandan jihar Yobe

Naira 25,000 ake bamu a matsayin kudin wata – Hukumar Yaki da Cutar Kanjamau ta Jihar Yobe

Babban Sakataren Hukumar Yaki da Cutar Kanjamau ta Jihar Yobe (YOSACA), Dokta Jibrin Adamu Damazal, ya ce rashin isassun kudade na daya daga cikin manyan kalubalen yaki da cutar kanjamau a jihar.

Naira 25,000 ake bamu a matsayin kudin wata – Hukumar Yaki da Cutar Kanjamau ta Jihar Yobe

Hukumar yaƙi da cutar sida ta jihar Yobe

Da yake jawabi yayin wani taron da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Damaturu don bikin ranar yaki da cutar kanjamau ta duniya 2024, Dakta Damazal ya bayyana cewa hukumar na karbar Naira 25,000 kacal a matsayin kason wata-wata, wanda ya bayyana a matsayin rashin wadatuwa wajen biyan bukatun aiki.

 

Ya jaddada cewa, kara yawan kudaden zai baiwa kungiyar YOSACA damar fadada shirye-shiryen da suka shafi marasa galihu kamar yara, matasa, da mata, da kuma tabbatar da dorewar kokarin yaki da cutar kanjamau.

Mataimakin Gwamna Mai Mala Buni, wanda ya wakilci Gwamna Idi Barde Gubana ya jaddada kudirin gwamnatin jihar na yaki da cutar kanjamau.

A cewar jaridar Daily trust Akalla mutane 2,934 ne ke dauke da cutar kanjamau a halin yanzu a fadin kananan hukumomi 13 na jihar Nasarawa, wanda hakan ya nuna an samu raguwa daga mutane 4,222 a shekarar 2023 da kuma 6,614 a shekarar 2022.

Babbar Daraktar Hukumar Yaki da Cutar Kanjamau ta Jihar Nasarawa (NASACA), Dakta Ruth Nabe-Bello, ce ta bayyana hakan a ranar Litinin din da ta gabata a yayin taron ranar yaki da cutar kanjamau ta duniya na shekarar 2024 a Lafia, babban birnin jihar.

Ta bayyana damuwarta game da kyama da nuna wariya da masu dauke da cutar kanjamau ke fuskanta a jihar, inda ta ce takaita hanyoyin samun kiwon lafiya musamman ga manyan al’umma, ya kasance wani lamari mai daukar hankali.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button