Uwargidan gwamnan Anambra ta ba da tallafin kayan agaji ga ‘yan gudun hijira.

Uwargidan gwamnan jihar Anambra, Dokta Nonye Soludo, a ranar Laraba, ta ziyarci makarantar Central, Odekpe a karamar hukumar Ogbaru ta jihar, inda a halin yanzu mutanen da ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu a yankin ke samun mafaka.

Spread the love

Wakilin jaridar Leadership ya tattaro cewa, a yanzu haka al’ummomin kananan hukumomi biyar na jihar ne ambaliyar ta shafa kuma sun hada da kananan hukumomin Anambra ta Yamma da Anambra ta Gabas da Ogbaru da Awka ta Arewa da kuma Ayamelum sakamakon ballewan ruwan daga kogin Neja.

gwamnatin jihar ta samar da sansanonin da bai gaza 27 ba, inda a halin yanzu wadanda ambaliyar ta shafa daga wadannan kananan hukumomin ke samun mafaka.

Yayin da yake jawabi ga mazauna sansanin da ke Odekpe, gomna Soludo ya ba su tabbacin cewa gwamnatin za ta yi duk abinda ya dace domin ganin an kula da su.

Haka kuma uwargidan gwamnan ta yi kira ga sauran masu hannu da shuni da su kai agaji wa wadanda ke cibiyoyin daban-daban a jihar ta Anambra

Ko’odinetan shiyyar Kudu maso Gabas na Hukumar Lafiya ta Duniya, Dokta Chukwumuanya Igboekwu, ya bayar da tabbacin cewa kungiyar za ta taimaka wa sansanin da asibitin tafi da gidanka da magunguna domin ba da kulawa na lafiya kyauta ga mazauna san sanin.

An kuma bayar da gudummawar kayayyakin abinci, da tufafi da kuma abubuwan sha da kudade ga cibiyoyin hudu da ke karamar hukumar Ogbaru.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button