Tsananin da ake ciki a Nijeriya ya kusa zuwa karshe – Tinubu

Spread the love

Tsananin da ake ciki a Nijeriya ya kusa zuwa karshe – Tinubu

 

Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ranar Litinin, ya amince cewa ‘yan Najeriya na fuskantar matsaloli, amma ya ba da tabbacin cewa nan ba da jimawa ba lamarin zai zo ƙarshe.

Yayin da Tinubu ya nanata cewa gwamnatinsa na ƙoƙarin dai dai ta al’amuran, ya kuma lura cewa mafita kan abinda ke faruwa zai samu ne idan anyi hakuri.

A nasa bangaren, gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya yaba da shugabancin Tinubu wadda ya ce ya na kokarin ganin an shawo kan matsalolin da ‘yan Najeriya su ke fama da su.

Tinubu wanda Sakataren Gwamnatin Tarayya Sanata George Akume da Gwamnan Legas suka wakilta ya yi jawabi a wajen bikin cika shekaru 70 na Shugaban Citadel Global Community, Fasto Tunde Bakare a Legas.

Akume ya ce: “Shugaban kasa ya yarda cewa ana shan wahala, amma a karshe za a sa mu mafita koyaushe. Kuma hanyoyin magance matsaloli masu sarkakiya ba za su taba zama nan take ba, amma muna kan hanya madaidaiciya.”

Shugaban ya kuma bayyana Fasto Bakare a matsayin jagora na gari kuma mai fafutukar ganin gaskiya wanda ya bar tambarin da ba za a taba mantawa da shi ba, ba kawai ga masu bin koyarwarsa ba, har ma da kasa baki daya.

“Na amince da kishin ku na ganin Najeriya ta gyaru, kasa mai adalci da kuma gwamnati na gari. Wannan biki shaida ce ta rayuwa mai ƙarfi da ƙarfin hali, na saƙo mai ƙarfi da faɗakarwa mara tsoro, zurfafa zurfafan sadaukarwar ku don ɗaga ɗan adam.

A nasa bangaren, Sanwo-Olu ya ce wadanda ke rike da mukaman gwamnati na bukatar addu’o’i, yana mai cewa “Lokaci ne mai wahala, amma ka ga mu ma mutane ne masu rauni.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button