Trump ya naɗa shugabar ma’aikatan fadar White House.

Spread the love

Zaɓaɓɓen shugaban Amurka, Donald Trump ya sanar da naɗin Susan Summerall Wiles, a matsayin shugabar ma’aikatan fadar White House, idan ya karɓi mulki a shekara mai zuwa.

Wata sanarwa da ya fitar ta ce Wiles ta taimaka mani wajen lashe zaɓe da kafa sabon tarihi a siyasar Amurka, kuma mace ce mai ilimi da ƙwazon aiki wadda ake mutumtawa a duniya baki ɗaya.

Ina da yaƙinin cewa za ta taimaka mani wajen dawo da martabar Amurka da kuma zama abin koyi.

Kwamitin karɓar mulki na Donald Trump yana aiki yanzu haka domin zaƙulo mutanen da za a naɗa shugabancin manyan sassan gwamnati 15, ciki harda sakataren harkokin waje da kum na tsaro.

An bayyana Susie Wiles a matsayin ƴar siyasa da ake jin tsoro sosai, kuma wadda ba kowa ne ya santa ba.

Cikin ƙasa da shekjara guda bayan ta shiga harkokin siyasa, Wiles ta samu shiga cikin tawagar yaƙin neman zaɓen Ronald Reagan, gabanin yaƙin zaɓen 1980.

Ta bayar da gagrumar gudunmuwa wajen sauya akalar siyasar jihar Florida.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button