Trump ya lashe zaben kasar Amurka
Kafofin yada labarai sun bayyana a ranar Laraba cewa, Donald Trump ya lashe zaben shugaban kasar Amurka, inda ya doke Kamala Harris.
Nasarar da jam’iyyar Republican ta samu, bayan daya daga cikin mafi girman kamfen a tarihin Amurka na zamani, ya kasance abin ban mamaki musamman idan aka yi la’akari da wani laifi da ba a taba ganin irinsa ba, yunkurin kisa na kusa-kusa, da gargadi daga wani tsohon shugaban ma’aikatan da ke yi masa lakabi da “fascist.”
“Nasara ce ta siyasa kamar yadda kasarmu ba ta taba gani ba,” cewar Trump a wani taro murnan lashe zaben a Florida.
Mataimakiyar shugaban kasa Harris, wanda ta shiga takara a watan Yuli bayan Shugaba Joe Biden ya sauka, ta gudanar da yakin neman zabe wanda ta bayyana wasu zarge zargen ta’addanci da Trump ya yi da amfani da kalaman nuna wariyar launin fata da jima’i.
Trump shi ne shugaban kasa na farko a cikin fiye da karni daya da ya lashe zabe wa’adi na biyu a ma ban bantan lokuta.
Shi ne kuma mutum daya tilo da aka zaba a matsayin wanda ake tuhuma da laifi – ya yin da ya fuskanci hukunci a wata kotun New York saboda zamba a ranar 26 ga Nuwamba.
Trump Yanzu yana da shekaru 78 yana kan hanyar karya wani tarihi a matsayin shugaban kasa mafi dadewa a lokacin mulkinsa, wanda ya zarce Biden, wanda zai sauka a watan Janairu yana da shekaru 82.
Wasu daga cikin kudurorin Kamala Haris sun hada da samar da hadin kai, da mai da hankali kan hakkin zubar da ciki, da gargadi game da barazanar da Trump ke yi ga dimokuradiyya.