Trump ya bai wa Elon Musk muƙami a gwamnatin Amurka
Zaɓaɓɓen Shugaban Amurka, Donald Trump, ya naɗa Elon Musk a matsayin shugaban sabuwar ma’aikatar inganta ayyukan gwamnati.
Kwamatin yaƙin neman zaɓen Trump wanda ya tabbatar da hakan ya kuma sanar da Vivek Ramaswamy, mai zuba jari a harkokin fasaha, domin yin aiki tare a gomnatin sa.
Kwamatin yaƙin neman zaɓen Trump wanda ya tabbatar da hakan ya kuma sanar da Vivek Ramaswamy, mai zuba jari a harkokin fasaha, domin yin aiki tare da Musk a ma’aikatar mai suna (Dogecoin).
An ruwaito cewa sunan sabuwar ma’aikatar ya yi kama da sunan kuɗin kirifto da Elon Musk ya fi so mai suna Dogecoin, kuma an ƙirƙire ta ne domin kawo ƙarshen wahalhalu a harkokin gwamnati.
Bayanai sun ce mutanen biyu za su riƙa bai wa Fadar White House ƙarƙashin gwamnatin Trump shawara ne kan yadda za a gudanar da manyan sauye-sauye, a cewar Trump.
Tun da farko, Trump ya sanar da naɗa mai gabatar da shiri a tashar talabijin ta Fox, Pete Hegseth, domin ya zama sakataren tsaro, sannan da John Ratcliffe shugaban hukumar leƙen asiri ta CIA.
An daɗe ana sa ran Musk, wanda ya fi kowa kuɗi a duniya, zai shiga gwamnatin ta Trump bayan ya bai wa kwamatin yaƙin neman zaɓensa maƙudan kuɗaɗe.
Ramaswamy ya nemi takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar Republican kafin daga baya ya janye kuma ya mara wa Trump baya.