Tinubu ya yi sauyi a shugabannin hukumar raya arewa maso yamma 2024

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi sauye-sauye a jerin shugabannin sabuwar Hukumar Raya Arewa maso Yamma da ya naɗa a bayan nan. A makon nan ne Shugaba Tinubu ya tura sabon jerin sunayen mambobin hukumar ta kula da ci gaban Arewa maso Yamma (NWDC) zuwa Majalisar Dattawa domin amincewa.

Spread the love

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi sauye-sauye a jerin shugabannin sabuwar Hukumar Raya Arewa maso Yamma da ya naɗa a bayan nan. A makon nan ne Shugaba Tinubu ya tura sabon jerin sunayen mambobin hukumar ta kula da ci gaban Arewa maso Yamma (NWDC) zuwa Majalisar Dattawa domin amincewa.

Tinubu ya yi sauyi a shugabannin hukumar raya arewa maso yamma
Tinubu

Trust radio ta rawaito cewa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi sauye-sauye a jerin shugabannin sabuwar Hukumar Raya Arewa maso Yamma da ya naɗa a bayan nan.

A makon nan ne Shugaba Tinubu ya tura sabon jerin sunayen mambobin hukumar ta kula da ci gaban Arewa maso Yamma (NWDC) zuwa Majalisar Dattawa domin amincewa.

A cikin sanarwar da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Juma’a, ya bayyana cewa an maye gurbin wasu daga cikin sunayen da aka fara turawa.

Shugaban da aka zaɓa yanzu shi ne Alhaji Lawal Sama’ila Abdullahi da ya maye gurbin Ambasada Haruna Ginsau, sai kuma Farfesa Abdullahi Shehu Ma’aji wanda zai ci gaba da riƙe muƙamin Darakta Janar.

Kazalika, Tinubu ya naɗa Emeka Atuma a matsayin Shugaban Hukumar Ci Gaban Kudu maso Gabas (SEDC), kuma ya tura sunayen wasu mambobin na NWDC daga yankuna daban-daban na Nijeriya.

Sabbin sunayen wakikai daga yankuna shida na ƙasar waɗanda za su zama mambobi a Hukumar ta NWDC sun haɗa da Chukwu Chijioke da Ahmed Mohammed da Injiniya Ahmed Rufai Timasaniyu da Macdonalds Michael Uyi da Yemi Ola sai kuma Honarabul Babatunde Dada.

 

Tinubu ya bai wa firaministan Indiya lambar yabo ta GCON

Tinubu ya bai wa firaministan Indiya lambar yabo ta GCON 2024
Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya karrama firaministan Indiya, Narendra Modi da lambar yabo ta biyu mafi daraja a ƙasar wato GCON.

Tinubu ya bayyana hakan ne a lokacin ganawa da Mista Modi a fadar gwamnatinsa da ke Villa a Abuja.

A ranar Asabar da daddare ne firaministan na Indiya ya isa Najeriya a wata ziyara ta kwana guda da zai yi a ƙasar

Shugaban na Najeriya ya ce ya bai wa Modi lambar girmamawar ce domin ”nuna godiyarmu ga Indiya a matsayin ƙawar Najeriya”.

Ziyarar Modin ita ce ta farko da wani firaministan Indiya ya kai wa Najeriya tun 2007, lokacin da Firaminitan na wancan lokaci Dakta Dr Manmohan Singh ya kai ƙasar.

Shugabannin biyu za su mayar da hankali a tattaunawrsu wajen ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙasashen biyu.

 

An kashe mutum biyu a birnin Odesa – Shugaban yankin

Shugaban yankin Odesa na Ukraine ya ce an kashe mutum biyu tare da raunata wani yaro mai shekara 17 a Odesa Oblast.

Oleh Kiper ya ce yanzu haka ana ci gaba da aiki domin maido da lantarki da ruwa a yankin da ke kudancin Ukraine.

Haka ma a yankin Dnipropetrovsk, shugaban sojin yankin, Serhiy Lysa ya ce an kashe wasu mutum biyu tare da raunata biyar a gundumar Nikopol.

 

wuceRasha ta ƙaddamar da hari mafi muni tun farkon Satumba kan Ukraine

An kwashe tsawon daren da ya gabata ana jin ƙarar amon sautin na’urorin ankararwa a faɗin Ukraine, yayin da Rasha ta ƙaddamar da hare-haren jirage marasa matuƙa a wasu sassan ƙasar.

Ukraine ta fuskanci hare-hare masu muni irin waɗannan, to amma wannan shi ne mafi muni da aka kai ƙasar tun farkon watan Satumba.

Ana ganin an kai harin kan tashar makamashin ƙasar – wadda ta ƙunshin manyan injinan samarwa da rarraba wutar lantaki a ƙasar.

A kudancin ƙasar, birnin Mykolaiv na daga cikin wuraren da hare-haren suka fi muni, inda mutum biyu suka mutu, da dama suka jikkata.

Haka ma birnin Odesa da ke gaɓar tekun Black Sea an fuskanci katsewar lantarki.

Sannan a babban birnin ƙasar, Kyiv, tarkacen makamai da jirage marasa matuƙan da aka kakkaɓo sun faɗa a wurare daban-daban, amma babu rahoton jikkata.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button