Tinubu Ya kaddamar da wani shirin da zai Samar da Haɗin kan Yan Najeriya.

Spread the love

A wani yunkuri na samar da hadin kai da zaman lafiya a tsakanin ‘yan kasa shugaba Bola Tinubu ya umurci hukumar babban birnin tarayya Abuja da ta inganta fannin fasaha, al’adu da yawon bude ido a Abuja babban birnin kasar.

Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike ne ya sanar da hakan a yayin bikin bude bikin fasaha da al’adu na Abuja na shekarar 2024 (ASOFEST).

Wike wanda ya samu wakilcin Ibrahim Aminu, ya jaddada cewa FCTA za ta himmatu wajen tallafawa shirye-shiryen da suka dace da manufar Shugaban kasa, musamman wadanda ke bikin al’adun gargajiya na Najeriya da kuma bayar da gudummawa ga ci gaban tattalin arziki.

Ya kuma bayyana kudirin gwamnatin na inganta kyawawan dabi’un al’adun Najeriya a duniya.

Ministan ya bayyana cewa bikin ya kasance wani dandali mai kima na koyon sana’o’i da samar da ayyukan yi, musamman matasa da mata.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button