Tinubu ya bai wa firaministan Indiya lambar yabo ta GCON
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya karrama firaministan Indiya, Narendra Modi da lambar yabo ta biyu mafi daraja a ƙasar wato GCON.
Tinubu ya bayyana hakan ne a lokacin ganawa da Mista Modi a fadar gwamnatinsa da ke Villa a Abuja.
A ranar Asabar da daddare ne firaministan na Indiya ya isa Najeriya a wata ziyara ta kwana guda da zai yi a ƙasar
Shugaban na Najeriya ya ce ya bai wa Modi lambar girmamawar ce domin ”nuna godiyarmu ga Indiya a matsayin ƙawar Najeriya”.
Ziyarar Modin ita ce ta farko da wani firaministan Indiya ya kai wa Najeriya tun 2007, lokacin da Firaminitan na wancan lokaci Dakta Dr Manmohan Singh ya kai ƙasar.
Shugabannin biyu za su mayar da hankali a tattaunawrsu wajen ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙasashen biyu.
An kashe mutum biyu a birnin Odesa – Shugaban yankin
Shugaban yankin Odesa na Ukraine ya ce an kashe mutum biyu tare da raunata wani yaro mai shekara 17 a Odesa Oblast.
Oleh Kiper ya ce yanzu haka ana ci gaba da aiki domin maido da lantarki da ruwa a yankin da ke kudancin Ukraine.
Haka ma a yankin Dnipropetrovsk, shugaban sojin yankin, Serhiy Lysa ya ce an kashe wasu mutum biyu tare da raunata biyar a gundumar Nikopol.
wuceRasha ta ƙaddamar da hari mafi muni tun farkon Satumba kan Ukraine
An kwashe tsawon daren da ya gabata ana jin ƙarar amon sautin na’urorin ankararwa a faɗin Ukraine, yayin da Rasha ta ƙaddamar da hare-haren jirage marasa matuƙa a wasu sassan ƙasar.
Ukraine ta fuskanci hare-hare masu muni irin waɗannan, to amma wannan shi ne mafi muni da aka kai ƙasar tun farkon watan Satumba.
Ana ganin an kai harin kan tashar makamashin ƙasar – wadda ta ƙunshin manyan injinan samarwa da rarraba wutar lantaki a ƙasar.
A kudancin ƙasar, birnin Mykolaiv na daga cikin wuraren da hare-haren suka fi muni, inda mutum biyu suka mutu, da dama suka jikkata.
Haka ma birnin Odesa da ke gaɓar tekun Black Sea an fuskanci katsewar lantarki.
Sannan a babban birnin ƙasar, Kyiv, tarkacen makamai da jirage marasa matuƙan da aka kakkaɓo sun faɗa a wurare daban-daban, amma babu rahoton jikkata.