Sojojin Najeriya sunyi luguden wuta akan ’yan ta’addan Lakurawa

Spread the love

Jiragen sojin Najeriya sun yi luguden wuta tare da halaka mayaƙan ƙasar waje da aka fi sani da Lakurwa a yayin da suke shirin kai wa fararen hula hari.

Mayaƙan na Lakurawa sun gamu da ajalinsu ne a  yankin Zangeku na Jihar Zamfara da ke iyaka da Jihar Kebbi.

Kazalika wasu ’yan bindiga daga gungun ɗan ta’adda Ado Aleiro sun mutu a yayin luguden wutan da jiragen soji suka yi wa sansanoninsu.

Kakakin Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya, Iya Komodo Olusola Akinboyewa, ya ce ’yan bindiga da Lakurawan sun gamu da ajalinsu ne bayan rundunar ta samu sahihan bayanai kafin ta ƙaddamar da hare-haren kan maɓoyansu.

Ya ce Ado Aleiro da yaransa sun sha luguden wuta ne a tsaunukan Tsaunin Asola da ke Ƙaramar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara.

Ya bayyana cewa mutane da dama da aka yi garkuwa da su sun samu tserewa daga sansanin ’yan bindigar a yayin harin jiragen sojin, zuwa Jihar Kebbi.

Iya Komodo ya ce harin ya ragargaza babban rumbun makaman Ado Aleiro da yaransa, lamarin da ya girgiza su matuƙa.

A baya-bayan nan dai mayaƙan ƙasashen waje da aka fi sani da Lakurawa sun addabi yankunan Sakkwato da Kebbi inda suka hallaka mutane da dama.

Wasu mayakan da ake zargin Lakurawa ne suka hallaka mutum 17 tare da jikkata wasu da dama bayan sace dabbobi a garin Mera da ke Ƙaramar Hukumar Augie a Jihar Kebbi.

Al’ummomin yankin Jihar Sakkwato sun koka da cewa mayaƙan na Lakurawa sun yi musu kaka-gida inda suke aiwatar da tsauraran dokokin Musulunci.

Sun kuma bayyana cewa Lakurawa na karɓar Zakka a hannunsu da karfin tsiya kuma suna yaudarar matasan yankin da kuɗi domin shiga aƙidarsu.

Haka kuma sun yi zargin cewa mayaƙan ne suka kai yawancin muggan hare-haren da aka kao wa jami’an tsaro a baya-bayan nan.

Hasali ma, ba sa ga-maciji da jami’an gwamnati, kuma suna tsaurara binciken baƙi da mutanen yankin da suka dawo daga bulaguro.

Bayan nan ne Hedikwatar Tsaro ta Nijeriya ta tabbatar da shigowar mayaƙan Nijeriya, waɗanda ta ce tana yin duk mai yiwuwa domin murƙushe su.


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button