Sojojin Najeriya sun gano maɓoyar Lakurawa, a jihohi 2 na Katsina da Zamfara

Sojojin Najeriya sun gano maɓoyar Lakurawa, a Katsina da Zamfara

Spread the love

Sojojin Najeriya sun gano tare da lalata sansanonin sabuwar kungiyar ta’addanci mai suna Lakurawa a yankin Jibia na Jihar Katsina da Tsafe a Jihar Zamfara ta hanyar wani aikin musamman mai suna “Operation Chase Lakurawa Out.”

Sojojin Najeriya sun gano maɓoyar Lakurawa, a Katsina da Zamfara
Sojojin Najeriya

Sojojin musamman da Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Musa, ya tura, sun isa Jihar Sokoto a ranar Alhamis domin tallafa wa ayyukan tsaro da ake gudanarwa.

A yayin ganawa da manema labarai a Jihar Sokoto a ranar Juma’a, Birgediya Janar Ibikunle Ajose, Kwamandan Runduna ta 8 ta Sojojin Najeriya kuma Kwamandan Sashen 2 na Operation Fasan Yanma, ya bayyana wannan ci gaba.

A cewar Daily trust Ajose ya tabbatar da cewa “Operation Chase Lakurawa Out,” wanda aka fara gudanarwa mako guda da ya gabata, ya cimma gagarumin nasara, ciki har da tsaftace dazuzzuka da lalata sansanonin ‘yan ta’adda da dama.

Don tabbatar da dorewar wadannan nasarori, Ajose ya sanar da cewa Babban Hafsan Tsaro ya tura Rundunar Tsaro da Ayyukan Musamman.

A Jihar Katsina, Birgediya Janar B.O. Omopariola, Kwamandan Runduna ta 17 ta Sojojin Najeriya, ya bayyana cewa fiye da kungiyoyin ‘yan bindiga 50 masu manufofi da dabaru daban-daban suna aiki a cikin jihar.

Labarai masu alaƙa 

‘Yan ta’addan Lakurawa sun tsere a Kebbi yayin da sojoji suka kai musu hari a maboyarsu


Spread the love

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button